Babu amfanin da Saraki ya taba yi wa APC –Lai Mohammed

Saraki da Ekweremadu Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Jam'iyyar dawa ta PDP ke shugabancin majalisar dattawa

Ministan watsa labarai da al'adu Alhaji Lai Muhammad ya ce fitar Sanata Bukola Saraki daga APC babu illar da za ta yi wa jam'iyyar a zaben 2019.

A wata sanarwa da ofishinsa ya fitar ranar Laraba, ministan ya ce APC ba ta taba amfana da shugabancin majalisar dattawan ba duk da kasancewarsa mamba na jam'iyyar.

"Idan da shugaban majalisar dattawa ba mamban APC ba ne, da gwamnatin da jam'iyyar ke jagoranta ba za ta sha wahalar da ta sha ba, ta la'akari da jinkirin amincewa da ksafin kudi da kuma mamyan mukaman gwamnati da sauransu.

A ranar Talata ne Sanata Bukola Saraki tare da gwamnansa na jihar Kwara suka sanar da sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa babbar jam'iyyar adawa ta PDP.

A sanarwar da ya fitar kan ficewarsa, Saraki ya jaddada matakinsa, inda ya ce fitar dole ya yi, saboda yadda wasu jiga-jigan APC suka rufe duk wata kofa ta tabbatar da zaman lafiya da hadin kai da kuma fahimtar juna a jam'iyyar.

Amma Lai Mohammed wanda jiharsa daya da Saraki, ya ce, "tun kafa gwamnati ana tafiya da Saraki ne kamar dan adawa, da gangan yake yin zagon kasa ga gwamnatin APC".

"Idan ba mu ci amfaninsa ba a matsayinsa na shugaban majalisar dattawa, to ba abin da muka rasa don mun rasa shi" in ji shi.

Duk da Saraki ya yi gwamnan jihar Kwara shekara takwas, amma Lai Mohammed ya yi ikirarin cewa fitarsa za ta kara wa APC karfi a jihar.

Guguwar ficewa daga jam'iyyar APC da ke mulki a Najeriya na ci gaba da kadawa, yayin da 'yan majalisa da gwamnoni ke ci gaba da fita jam'iyyar.

A ranar Laraba ne gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya sanar da fita daga jam'iyyar APC zuwa PDP, wannan kuma ya biyo bayan fitar shugaban majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki da kuma wasu 'yan majalisa sama da hamsin.

Labarai masu alaka