Shugabar New Zealand Jacinda Ardern ta koma bakin aiki

Firai ministar New Zealand Jacinda Ardern Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Jacinda Adern

Firai ministan New Zealand Jacinda Ardern ta koma bakin aiki bayan hutun haihuwa na makonni shida da ta dauka .

Madam Ardern, mai shekara 38, ta haifi diyarta ta fari a watan Yunin da ya gabata , abinda ya sa ta zamo shugabar kasa ta biyu da ta haihu yayin da ta ke kan mulki.

A ranar Asabar ta fitar da wani hoton bidiyo a shafin Facebook inda ta bayyanna abubuwan da za ta yi a makonta na farko da komawa aiki.

Madam Ardern ta mika ragamar mulki ga mataimakinta , Winston Peters.

"Zan mayar da hankali gaya a kan aikina ," In ji Ms Ardern a cikin bidiyon da ta wallafa a shafin Facebook.

A ranar 21 ga watan Yuni ta haifi diyarta ta fari, da aka rada wa suna Neve Gayford.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Jacinda Adern da jaririyarta

Firai ministar ta cigaba da duba takardun Majalisar zartarwa kuma an rinka tuntubar ta kan wasu batutuwa masu muhimanci lokacin da ta ke hutu.

Madam Ardern, wadda aka zaba a watan Oktoban bara , ta sanar a watan Janairu cewa ita da abokin zamanta Clarke Gayford za su samu karuwa nan ba da jimawa ba.

"Ba ni ce mace ta farko da take abubuwa na komai da ruwanka ba. Ba ni ce mace ta farko mai jaririya da ke aiki ba - akwai mata da dama da suka yi haka a baya ." in ji ta

Ita ce shugabaar kasa mafi kankantar shekaru da aka samu a kasar tun bayan shekarar 1856.

A 1990 marigayiya Benazir Bhutto ta haifi yarta mace lokacin da ta ke rike da mukamin firai minista a Pakistan, wadda ya sa ta zama shugabar kasa ta farko a duniya da ta haihu kan mulki .

Labarai masu alaka

Karin bayani