Yadda rashin bayar da nonon uwa ke kashe jarirai

Yaran da aka fara ba su nonon uwa da wuri sun fi samun ingantacciyar rayuwa Hakkin mallakar hoto Getty Images

Majalisar Dinkin Duniya ta ce wani kiyasi ya ce jariri miliyan 78 sabbin haihuwa ne cikin mummunan hadarin mutuwa duk shekara saboda rashin samun nonon uwa cikin sa'o'in farko na zuwa duniya.

Wani sabon rahoto da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta wallafa tare da hadin guiwar Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Duniya, domin ya zo daidai da farkon makon wayar da kan al'umma kan shayar da jarirai nonon uwa zalla, ya yi nazari kan iyaye mata a cikin kasashe 76 da ke da matsakaici da kuma karamin karfi.

Inda ya gano cewa biyu ne kadai cikin jariri biyar ke samun nonon uwa da zarar an haiho su a duniya.

Rahoton ya nuna cewa yaran da aka bai wa nonon uwa cikin sa'a ta farko bayan haihuwa sun fi samun damar rayuwa.

Sannan kuma yin jinkiri na sa'o'i kadan bayan haihuwa na iya saka rayuwar sabbin haihuwa cikin hadari.

Bugu da kari dora jinjiri kan jikin mahaifiyarsa da saka masa kan nonon uwa a bakinsa sukan zaburar da gabobin da ke samar da nono ga jinjiri, da kuma madarar farko da yaro kan tsotsa wadda ke da matukar amfani ga lafiyarsa ta hanyar ba shi kariya daga cututtuka.

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya Dr Tedros Adhanom ya ce nonon uwa na sanyawa jariri ya fara rayuwa mafi inganci tun daga lokacin haihuwa.