Zaben Zimbabwe ya bar baya da kura

People queuing to vote

Matakin da gwamnati ta dauka na murkushe masu zanga-zanga bayan zaben da aka gudanar ranar Litinin a Zimbabwe, ya janyo kasashen duniya na cewa a yi taka-tsan-tsan.

Majalisar Dinkin Duniya da tsohuwar kasar da ta yi Zimbabwe mulkin mallaka wato Birtaniya, sun bayyana damuwarsu a kan rikicin, inda mutum uku suka mutu sakamakon bude musu wuta da dakaru suka yi.

Jam'iyyar Zanu-PF ce ta yi nasara a sakamakon zabukan 'yan majalisu, a kuri'un farko da aka kada tun bayantsige tsohon shugaban kasar Robert Mugabe da ya shafe shekaru masu yawa a kan mulki.

Amma jam'iyyar adawa ta ce Zanu-PF ta yi magudi a zaben.

Har yanzu ba a sanar da sakamakon zaben shugaban kasa ba.

Jam'iyyar adawa ta ADC ta jajirce cewa dan takararta, Nelson Chamisa ne ya yi nasara a kan Shugaba Emmerson Mnangagwa.

Jam'iyyar Zanu-PF wacce ta shafe shekara 38 a mulki, tun bayan da kasar da ta samu 'yancin kai, ta yi watsi da cewa ta yi magudi, sannan kuma ta yi kira da a zauna lafiya.

Shugaba Mnangagwa ya ce yana tattaunawa da Mista Chamisa don dakile rikicin kuma "dole mu cigaba da wannan tataunawar domin mu tabbatar da dorewar zaman lafiyar da muke so."

A wasu jerin sakonnin Tiwtter, ya ce yana son a gudanar da bincike mai zaman kansa don tabbatar da cewa an gurfanar da masu hannu a tashin hankalin gaban shari'a.

Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya yi kira ga 'yan siyasar Zimbabwe su yi taka tsan-tsan, yayin da ministar harkokin wajen Birtaniya, Harriett Baldwin ta ce "ta damu matuka" da tashin hankalin.

Ofishin jakadancin Amurka a Harare ya yi kira ga sojojin da su yi taka tsan-tsan, yana mai cewa kasar tana da "fatan" samun cigaba mai kyau nan gaba.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Magoya bayan jam'iyyar adawa sun yi fushi da sakamakon kuma sun kasa yarda da hukumar zabe

Mukaddashin Sakatare Janar na kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International Colm O Cuanachain, a wata sanarwa ya ce, amfani da karfin soji a rikicin bayan zaben, "yi wa 'yancin fadin albarkacin baki dabaibayi ne da kuma 'yancin gudanar da taruka."

"Dole a bai wa mutane damarsu ta yin zanga-zanga," in ji shi.

Rahotanni sun ce ba a cigaba da tashin hankalin ba a ranar Alhamis. Wata babbar mota cike da 'yan sanda da sojoji na ta yawo a cikin birnin, suna ihun ce: "Ku shiga taitayinku 'yan Zimbabwe."

Me ya faru bayan zaben?

Shugaban hukumar zaben kasar ya ce jam'iyyar Zanu-PF ta samu nasara da kashi biyu cikin uku na majalisar dokoki - abun da ya jawo tashin hankali a babban birnin Harare.

Ministan harkokin cikin gida Obert Mpofu ya ce gwamnati ba za ta dauki zanga-zangar da ake yi ba.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sojoji sun bude wuta don tarwatsa masu zanga-zanga
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jami'an 'yan sanda sun bazu a kan titunan babban birnin

'Yan hamayya "suna gwada jajircewarmu", in ji shi, "ina ganin suna wani babban kuskure."

Wani mai magana da yawun Mista Chamisa ya yi tir da girke sojoji da kuma rasa rayukan da aka yi daga baya.

Ya ce "An horas da sojoji ne domin kisa a lokacin yaki. Shin fararen hula makiyan kasa ne?

"Babu irin bayanin da za a iya kafa hujja da shi game da wannan cin zarafin."

Wane sakamako ne aka fitar?

Kawo yanzu dai hukumar zaben Zimbabwe ta bayar da sanarwar nasarar da jam'iyyar Zanu-PF ta yi a kujeru 140, inda MDC Alliance ta samu 58, kamar yadda kafar watsa labaran ZBC mallakar kasar ta ruwaito.

Akwai kujeru 210 a majalisar dokokin kasar.

An yi wa sama da mutum miliyan biyar rijistar zabe, kuma kashi 70 cikin 100 sun fito zabe.

ZBC ta bayar da rahoton cewar hukumar zaben kasar za ta bayyana sakamakon zaben shugaban kasa da misalin karsfe 12:30 agogon kasar (kuma karfe 10:30 agogon GMT) ranar Laraba, amma sakamakon zabukan majalisar dokoki kawai aka bayyana.

Wakiliyar BBC, Shingai Nyoka, ta bayar da rahoton cewar ba a fitar da sakamakon zaben shugaban kasar ba domin wakilan 'yan takara 23 ba su zo sun tantance sakamakon ba.

Kowane dan takara yana bukatar sama da kashi 50 cikin 100 domin yin nasara kai tsaye a zaben. Idan ba haka ba, sai an yi zaben zageye na biyu ranar 8 ga watan Satumba.

Mene ne masu sa ido a zabe ke cewa?

Masu sa ido daga kungiyar Tarayyar sun soki jinkirin da aka yi wajen bayyana sakamakon zaben shugaban kasa. ZEC tana da lokaci zuwa ranar Asabar ta bayyana sakamakon.

Kungiyar masu sa idon ta ce ta ga matsaloli daban-daban ciki har da son kai na kafafen yada labarai, barazana ga masu zabe da kuma rashin yarda a hukumar zaben kasar, tana mai karawa da cewar "ingantaccen yanayin siyasa, da kuma rashin adalci da rashin aminci."

Wannan shi ne karon farko cikin shekara 16 da gwamnatin ta kyale masu sa ido a zabe daga Turai da Amurka su shiga kasar.

Kungiyar masu sa ido ta Kungiyar Tarayyar Afirka ta ce "an yi zabukan cikin yanayi na lumana".

Labarai masu alaka