Kwale-kwale ya yi ajalin 'yan gudun hijira 21 a Sokoto

People crowd a small boat in Lagos Hakkin mallakar hoto Getty Images

Mutum 21 sun rasa rayukansu bayan da wani kwale-kwale ya yi hadari a jihar Sakkwato a safiyar ranar Alhamis.

Hukumomi a jihar sun ce hadarin ya faru ne a kogin Gandi kuma cikin mutanen da suka rasa rayukansu akwai mata 17 da kuma yara hudu.

Mutanen suna kan hanyarsu ce ta zuwa kauyensu mai suna Gidan-Kari yayin da kwale-kwalen ya kife a kogin.

Sai dai akwai kimanin mutum 10 wadanda suka tsira da ransu bayan hadarin.

Mutanen 'yan gudun hijira ne da rikici jihar Zamfara ya raba da muhallansu kuma suna kan hanyarsu ta koma wa gida ne, kamar yadda wani jami'in hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar (SEMA) ya shaida wa BBC .

Sai dai ba a bayyana dalilin da ya jawo hadarin ba tukunna, amma ana yawan samun hadarin kwale-kwale saboda dibar mutane fiye da kima da yawan torokon ruwa da rashin kula da jiragen ruwan yadda ya kamata da kuma rashin kyauwun kogunan da suke bi.

Labarai masu alaka