Kare ya kashe yar shekara daya a Australia

Motocin 'yan sanda da motar daukar marasa lafiya a wajen gidan da lamarin ya faru Hakkin mallakar hoto AUSTRALIAN BROADCASTING CORP
Image caption Karen ya kai wa yarinyar hari ne a gidansu da ke Victoria.

Wata yarinya mai shekara daya ta rasu bayan wani kare ya kai mata hari a Ostraliya, in ji 'yan sanda.

Karen ya farwa yarinyar ne inda ya rika cizonta a wani gida da ke unguwar Neerin Junction a gabashin garin Melbourne da ke jihar Victoria..

An kira 'yan sanda da ma'aikatan jinya zuwa gidan da safiyar ranar Laraba sai dai sun kasa farfado da yarinyar .

Kafofin watsa labarai a Ostraliya sun ce karen ya farwa yarinyar ne a fuska.

Mahaifiyar yarinyar ta yi kokarin kubatar da yarta daga hannun karen amma hakarta ba ta cimma ruwa ba in ji kafar watsa labarai ta Seven News.

'Yan sanda sun ce tuni jamian karamar hukuma suka kwace karen domin tsare

Labarai masu alaka