Emerson Mnangagwa ya lashe zaben Zimbabwe

Shugaban kasa mai ci a yanzu ya lashe zaben Zimbabwe Hakkin mallakar hoto AFP/GETTY
Image caption Emerson Mnagagwa

Shugabar hukumar zaben Zimbabwe, justice Priscilla Chigumba ta bayyana shugaban kasa mai ci a yanzu, Emerson Mnangagwa a matsayin wanda ya yi nasara a zaben shugaban kasar .

Mr Mnangagwa ya yi nasara da kashi 51 na kuri'un da aka kirga, a kan abokin hamayyarsa Nelson Chamisa, wanda ya samu kashi 44 na kuri'u.

Shugaba Mnangagwa ya lashe shida daga cikin larduna goma da ke kasar, yayin da Nelson Chamisa na jamiyyar adawa ta MDC ya lashe larduna 4.

'Yan sanda sun fitar da jami'an yan adawa daga cikin dakin tattara sakamakon zabe lokacin da suka ki amincewa da sakamakon.

Shugaban jamiyyar adawa ta MDC ya yi watsi da sakamakon zaben, inda ya ce sakamakon karya ne kuma ba a tantance shi ba.

Mr Mnangagwa ya kauce ma zagaye na biyu na zabe tsakaninsa da Mr Chamisa, saboda ya samu kashi 50 cikin dari na kuri'u.

Sai dai Mr Chamisa ya nanata cewa shi ne ya lashe zaben, inda ya fada wa 'yan jarida a ranar Alhamis cewa jamiyyar Zanu PF mai mulki na kokarin "sauya sakamakon zabe" kuma abu ne da ba "za su lamunta da shi ba".

Sai dai hukumar zaben kasar ta musanta zargin tafka magudin zabe.

Labarai masu alaka