Tafiyar Buhari Landan makarkashiya ce – PDP

Muhammadu Buhari zai yi hutun kwana goma daga 3 ga watan Agusta Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Buhari zai fara hutunsa ne a ranar Juma'a

Jam'iyyar PDP a Najeriya ta yi zargin cewa tafiyar Shugaba Muhammadu Buhari hutun kwana 10 a Landan, wani shiri ne na tsame shi daga makarkashiyar da jam'iyyar APC mai mulki ta tsara na yin kutse da aikata ba daidai ba a majalisar dokokin kasar.

Sanarwar da Sakataren yada labaran jam'iyyar na kasa, Kola Ologbondiyan ya fitar ta ce PDP na sane da makarkashiyar da aka kitsa a wani taro ranar Laraba.

"Tsakanin fadar shugaban kasa da sanatocin APC, na sake bude majalisa ala tilas tare da rakiyar jami'an tsaro da nufin tsige Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki da mataimakinsa Ike Ekweremadu," in ji shi.

Sai dai mai taimakawa shugaban kasar kan yada labarai Malam Garba Shehu ya musanta zargin a wata hira da yi da sashen BBC Pidgin.

A wata sanarwa da fadar shugaban Najeriya ta fitar, ta nuna cewa tuni Muhammadu Buhari ya aika da takarda ga shugaban majalisar dattawa da kuma na majalisar wakilan kasar domin sanar da su game da hutun wanda zai fara ranar Juma'a.

Wannan zargi da PDP din ke yi ya zo ne bayan da wasu daga cikin sanatoci, da suka hada har da Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki suka sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa PDP.

Tun bayan sauya shekara da Bukola Saraki ya yi, ana ta muhawara kan matsayin shugabancinsa a majalisar, a lokacin da jam'iyyun biyu ke jayayya kan wadda ta fi yawan wakilai a majalisar.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Ana ganin cewa sanatocin jam'iyyar APC za su so mukamin ya koma a hannunsu.

A wata hira da ya yi da BBC, Sanata Ali Ndume na jam'iyyar APC, ya ce zai yi kyau Saraki "ya ajiye mukamin da kansa, ba tare da bari sai an tursasa masa ba."

Shi ma shugaban jam'iyyar APC na kasa Adams Oshiomole, a wata hira da ya yi da manema labarai, ya ce kamata ya yi Saraki ya ajiye mukaminsa tun da dai ya bar jam'iyyar APC.

A yanzu haka dai, shugaban Majalisar datijai Bukola Saraki, da mataimakinsa Ike Ekwerenmadu dukkaninsu 'ya'yan jam'iyyar PDP ne.