'Yanzu PDP ta fi APC karfi a majalisar dattawa'

Dogara da Amechi da Wamakko
Image caption Dogara da Amaechi da Wamakko ba su fice daga jam'iyyar APC ba

Cikin 'yan makwannin nan ne dai wasu daga cikin jigajigan 'yan siyasa a Najeriya da ke kiran kansu 'yan sabuwar jam'iyyar PDP suka fita daga jam'iyyar APC mai mulki.

Komawarsu jam'iyyar APC na cikin dalilan da suka bai wa jam'iyyar nasara a zaben 2015.

Yayin da wasu masharhanta ke ganin tarihi ne yake son maimaita kansa, ya kamata a san adadin 'yan sabuwar PDP din da suka bar jam'iyya mai mulki din da kuma wadanda ba su bar jam'iyyar ba.

Tun karshen shekarar 2013 ne dai wasu 'yan majalisar wakilai 37 suka sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa jam'iyyar APC.

Cikin wadannan 'yan majalisu 37 na wancan lokacin, akwai Yakubu Dogara daga jihar Bauchi.

Kafin zaben 2015, guguwar sauya shekar ta fara ne da ficewar gwamnoni biyar daga bangaren sabuwar PDP zuwa APC, kafin 'yan majalisar su sauya sheka.

Gwamnonin sabuwar PDP din da suka fice sun hada da gwamna Rabiu Musa Kwankwaso na jihar Kano da Murtala Nyako na jihar Adamawa da Aliyu Magatakarda Wamakko na jihar Sokoto da Rotimi Chibuike Amaechi na jihar Ribas da kuma Abdulfatah Ahmed na jihar Kwara.

Gwamnoni biyu daga cikin 'yan sabuwar PDP ne kawai ba su fice daga jam'iyyar ba, wato Gwamna Mu'azu Babangida Aliyu na jihar Neja da Sule Lamido na jihar Jigawa.

Kuma a watan Janairun 2014 ne dai 'yan majalisar dattawa 11 suka sauya sheka daga sabuwar PDP din zuwa APC.

Hakkin mallakar hoto TWITTER/EFFC
Image caption Attahiru Bafarawa na cikin wadanda suka kafa APC, amma ya fice daga jam'iyyar gabannin zaben shekarar 2015

'Yan majalisar sun hada da Bukola Saraki da ke wakiltar jihar Kwara ta tsakiya da Umaru Dahiru da ke wakiltar jihar Sokoto ta kudu da dai sauransu.

Ba 'yan sabuwar PDP ne kawai suka sauya sheka daga PDP ba a wancan lokacin.

Ministan kasuwanci a gwamnatin tsohon Shugaba Jonathan, Samuel Ortom ya fice daga PDP zuwa APC daf da zaben 2015.

A zaben na shekarar 2015 ya zama gwamnan jihar Benue.

Amma a wancan lokacin ne tsoffin gwamnonin jihar Sokoto da na Kano, Attahiru Bafarawa da Ibrahim Shekarau, suka sauya sheka daga APC din PDP.

Bayan kimanin shekara biyar da aka yi guguwar sauya sheka daga PDP, yanzu kuma guguwar ta sake kadawa inda wasunsu ke fita daga APC zuwa inda suka fito.

A cikin wadanda suka sauye shekar daga APC, akwai tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso wanda ya sauya sheka daga APC zuwa PDP.

Gwamnan jihar Kwara, Abdulfatah Ahmed ya sauya sheka daga APC zuwa jam'iyyar PDD tare da shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, da kakakin jam'iiyar APC, Bolaji Abdullahi.

Tsohon gwamnan jihar Adamawa, Murtala Nyako da dansa, Abdul-Azeez Nyako sun sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa jam'iyyar ADC.

Gwamna Samuel Ortom na jihar Binuwe ma ya sauye sheka daga APC zuwa PDP.

Su wasuka rage a APC?

Shugaban majalisar wakilai Hon Yakubu Dogara yana cikin wadanda suka shigo APC daga PDP, kuma wasu na ganin yana kan hanyar fita daga jam'iyyar duk da cewa bai fito ya nuna zai fita ba kawo yanzu.

Amma kusancin da ke tsakanin shi da Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki, wasu ke ganin yana tare da PDP, ko da kuwa har yanzu yana ci gaba da zama a APC bai fita ba.

Sannan akwai wasu tsoffin gwamnoni da ba su sauya sheka ba cikin gwamnonin da suka koma APC daga sabuwar PDP.

Tsoffin gwamnonin sun hada da ministan sufurin Najeriya, Rotimi Chibuike Amaechi wanda ya jagoranci yakin neman zaben shugaba Buhari a zaben 2015. amma wasu na ganin don ana damawa da shi a gwamnatin APC da ke mulki, ba ya cikin lissafin 'yan sabuwar PDP da ake ganin za su fice daga APC.

Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, ya ce yana nan daram dam a APC, duk da gwamnansa Aminu Waziri Tambuwal ya fita daga jam'iyyar da a karkashinta aka zabe shi.

Hakkin mallakar hoto .
Image caption Jam'iyyar APC dai tana ganin ficewar 'yan sabuwar PDP din ba za ta hana ta lashe zabukan da kasar ke fuskanta ba

Wa ya fi rinjaye a majalisa?

Image caption Yanzu dai majalisar wakilai da ta dattawa na hutun makwanni

Batun jam'iyyar da ta fi rinjaye a majalisun dai wani abu ne da ake ganin shi ne ma fi muhimmanci a wannan al'amari.

A yanzu dai 'yar manuniya ta nuna cewa jam'iyyar APC ce ke da rinjaye a majalisar dattawan kasar inda ta fi PDP da mutum 1 bayan ficewar shugaban majalisar Bukola Saraki.

Jerin sunayen jiga-jigan da suka sauya sheka daga APC zuwa yanzu

Hakkin mallakar hoto .
Image caption Wadannan na cikin 'yan majalisar dattawan da suka sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa PDP

Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki

Gwamnan jihar Sokoto Aminu Tambuwal

Kakakin jam'iyyar APC Bolaji Abdullahi Ahmed

Jakadan Najeriya a Afirka Ta Kudu, Ahmed Ibeto

Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom

'Yan majalisar dokoki ta kasa fiye da 50 sun sauya sheka daga APC zuwa PDP da suka hada da Kwankwaso da Hunkuyi da Melaye da Hamma Misau da Nazif Gamawa da sauran su

Bangaren Akida da Restoration a jihar Kaduna wadanda ke rigima da Gwamna Nasir el-Rufa'i

Bangaren rAPC na Buba Galadima ya kulla alaka da PDP domin kayar da APC a 2019 - wasu na ganin su ma sun kama hanyar ficewa daga jam'iyyar

Sanata Abdul-Azeez Nyako da Dan majalisar Wakilai Rufai Umar daga Adamawa sun koma jam'iyyar ADC

Hakeem Baba Ahmed - shugaban ma'aikata a ofishin Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki

Usman Bawa - mataimaki na musamman ga Kakakin Majalisar Wakilai Yakubu Dogara.

Wanne tasiri sauyin shekar zai yi?

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Idayat Hassan, Darakta ce a Cibiyar Demukradiyya da Ci-gaba (CDD), kuma mai sharhi kan al'amuran siyasa, ta ce a yanzu PDP ta kara samun tagomashi a majalisar dokokin kasar.

"Dama can jam'iyya mai mulki na fuskantar tarnaki wajen gabatar da sabbin dokoki: alal misali ana daukar lokaci kafin a fitar da kasafin kudi.

"Wannan abu da ya faru na nufin APC tana cikin tsananin rikici saboda a yanzu zai yi wa mutane wahala su hade waje daya.

"Sannan abubuwa kamar girke 'yan sanda a kofar gidajen shugaban majalisar dattawa da mataimakinsa abu ne da ka iya batawa gwamnati suna, saboda ya yi kama da bi-ta-da-kullin siyasa.A ganin Idayat Hassan, a yanzu tsige shugaban kasa abu ne mai yiwuwa, "Matakai ne masu sarkakiya, kuma da wuya hakan ta faru cikin wata shida kafin babban zabe, amma 'yan adawa za su iya taso da maganar don aika wani sako," in ji ta.

Shi ma Farfesa Jibrin Ibrahim ya ce a yanzu ba za a iya sanin tasirin sauyin shekar ba, dalili shi ne a APC an san Buhari ne zai yi takara amma ba a san dan takarar PDP.

"Sai an san waye dan takarar PDP sannan za a san ko zai iya takara da Buhari ko ba zai iya ba."