Pedro ya tsawaita zamansa a Chelsea

Pedro ya shiga kungiyar Chelsea a 2015 Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Pedro ya shiga kungiyar Chelsea a 2015

Dan wasan Chelsea Pedro ya sanya hannu kan yarjejeniyar kwangilarsa wadda za ta kara masa shekara daya a Stamford Bridge inda zai kai har shekarar 2020.

Pedro, mai shekaru 31, ya koma kungiyar ne daga Barcelona a shekarar 2015 a kan fam milliyan 21.

Dan kwallon kuma ya taimaka wa kulob din lashe gasar Premier ta 2016-17 da kuma gasar cin kofin FA ta bara.

Dan kwallon na Spain ya zura kwallaye 28 a wasanni 131 kuma ya zura kwallaye yayin da kungiyarsa ta yi wasan share fage da kungiyar Perth Glory da kuma Inter Milan.

"Ina jin dadi a nan kuma ina so in lashe sabbin kambuna da kofuna", in ji Pedro, wanda ya yi kakar wasa tara a Barcelona kawo yanzu.

Labarai masu alaka

Labaran BBC

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba