Dan kirki ne aka mayar da shi mai tsattsauran ra'ayi – Mahaifiyar Osama

Image of smiling Osama bin Laden with firearm in background Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An dora alhakin hare-haren ta'addanci na 11 ga watan Satumba a Amurka har ma wasu a sassan duniya kan kungiyar da ya jagoranta

Mahaifiyar marigayi Osama Bin Laden, wanda ya shugabanci kungiyar al Qaeda ta yi magana a karon farko shekaru bakwai bayan mutuwarsa a 2011.

Alia Ghanem ta yi hira da jaridar Guardian ta Birtaniya daga gidansu da ke birnin Jidda a kasar Saudiyya.

Ta fada ma jaridar cewa dan nata mai kunya ne kuma mai kyawawan halaye a lokacin da yake tasowa, amma daga baya ta ce an juya masa tunani a jami'a.

Iyalansa sun ce a shekarar 1999 ne suka yi tozali da shi a karo na karshe, shekara biyu kafin harin 11 ga watan Satumba a lokacin yana Afghanistan.

"Batun ya tayar mana da hankali matuka. Ban so irin wannan abin ya faru ba. Saboda me yayi watsi da tayuwarsa baki daya? inji uwargida Ghanem da aka tambayeta yay ta ji da aka ce dan nata ya zama dan gwagwarmayar addinin Islama?

Iyalan Bin Laden na da karfin fada a ji a kasar saudiyya, bayan da suka tara makudan kudade daga harkar gine-gine.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sojojin Amurka sun kashe Bin Laden daga baya a wani gida da ke Abbottabad cikin Pakistan

Mahaifin Bin Laden Mohammed bin Awad bin Laden ya saki Alia Ghanem shekara uku bayan an haifi Osama, kuma 'ya'yansa sun kai 50.

Bayan harin 9 ga watan Satumba, iyalan Bin Laden sun ce hukumomin Saudiyya sun yi ta masu tambayoyi, kuma daga baya an takaita masu tafiye-tafiye.

Dan jaridan da ya gudanar da ganawar, Martin Chulov ya ce Saudiyyar ta kyale shi yayi wannan hirar da uwargida Alia Ghanem ne saboda duniya ta shaida cewa Osama fandararre ne a cikin dangi.

Ya ce wannan kuma dama ce ta nuna cewa Osama ba yana ma daular Saudiyya aiki ba ne, kamar yadda wasu ke ikirari.

'Yan uwan Osama su biyu Hasaan da Ahmad sun halarci wannan hirar da jaridar Guardina din ta yi, kuma suma sun bayyana tashin hankalin da suka shiga da aka sanar da su cewa Osama na da hannu wajen kai hare-haren na 11 ga watan Satumba.

"Dukkanmu babba da yaro mun ji kunyar wannan abin da yayi. Mun kuma san cewa zamu dandana kudarmu. Iyalan gidanmu da ke kasashen waje duk sun dawo gida", Ahmad ya fada ma jaridar.

Ya kuma ce har yanzu mahaifiyarsu na dora laifin Osama kan wasu mutanen, maimakon a kansa.


Rayuwar Bin Laden

Hakkin mallakar hoto AFP
  • 1957: An haife shi a birnin Riyadh na Saudiyya. Iyayensa sun rabu kuma mahaifinsa ya mutu a wani hadarin jirgi mai saukar angulu a 1969. Ya yi karatu a Jidda kafin ya tafi Afghanistan inda ya shiga yaki da tarayyar Soviet kuma ya hada tasa rundunar
  • 1988: Ya samar da kungiyar al-Qaeda mai ma'anar "cibiya'
  • 1989: Ya koma Saudiyya bayan janyewar sojin tarayyar Soviet. Amma an kore shi daga kasar, sai shi da magoya bayansa suka koma Sudan, kana ya koma Afghnaistan daga can
  • 1993: 'Yan uwansa sun kore shi daga cikin masu hannun jari a kamfanonin gidan, kuma gwamnatin Saudiyya ta soke damarsa ta zama dan Saudiyya
  • 1996: Ya ayyana yaki kan sojojin Amurka
  • 1998: Ya fitar da wata fatawa ta halasta kisan Amurkawa da Yahudawa a fadin duniya. An dora laifin hare-haren da aka kai a ofisoshin jakadancin Amurka a Nairobi da Dar es Salam kan kungiyarsa ta al Qaeda. Daga nan ya fara buya kuma ya rika tashi zuwa wani sabon wuri domin kauce wa farmaki
  • 2000: An kashe sojojin Amurka 17 a wani hari da aka kai kan jirgin ruwan yaki na Amurka USS Cole a tashar jirgin ruwa ta Yemen
  • 2001: Jiragen sama hudu na fasinja da magoya bayansa su 19 suka kwace sun kai hare-hare akancibiyar ciniki ta New York, World Trade Centre da ma'aikatar tsaron Amurka Pentagon. Daya daga cikinsu ya fadi a Pennsylvania inda dukkan fasinjojinsa suka mutu. Kusan mutum 3,000 ne suka mutu a ranar. Shugaban Amurka na wancan lokacin George W Bush ya ce Amurka na neman Bin Laden "da rai ko a mace", kuma ya kai ma Afghanistan hari a sanadiyyar haka
  • 2002-2010: An yi hasashen ya tsere zuwa cikin Pakistan a shekara 2001. al Qaeda ta rika sakin hotunan bidiyonsa jefi-jefi
  • 2011: Sojin Amurka na Navy Seals sun kai wani hari a gidan da yake zama a garin Abbottabad na Pakistan kuma sun kashe shi. An kashe wasu mutum hudu a cikin gidan tare da shi. Sojjoin sun birne shi a teku bayan an yi masa sallar jana'iza a kan wani jirgin ruwan yaki na Amurka

Labarai masu alaka