Mutum 18 sun mutu a hatsarin jirgi mai saukar angulu a Rasha

Handout photo showing two MI-8 helicopters belonging to Utair Hakkin mallakar hoto EPA/HELI.UTAIR.RU
Image caption Hoton irin jirgin mai saukar angulu samfurin MI-8 mallakin kamfanin Utair da ya fadi

Mutum 18 sun mutu a wani hatsarin jirgin mai saukar angulu a yankin arewa maso yammacin Saiberiya na kasar Rasha, kamar yadda jami'ai daga yankin suka bayyana.

Jami'ai masu bayar da taimakon gaggawa sun ce jirgin samfurin MI-8 ya fadi ne da karfe 10 da minti 20 agogon yankin (karfe 3:20 agogon GMT) kimanin kilomita 180 daga garin Igarka da ke yankin Krasnoyarsk.

Dukkan wadanda ke cikin jirgin sun mutu - akwai matuka jirgin su uku da fasinjoji 15.

Jirgin na kan hanyarsa ta jigilar ma'aikata masu aiki a wata tashar da ake hako man fetur ne, kuma jami'an 'yan sanda sun fara gudanar da bincike.

Bayanan farko sun ce farfelolin jirgin sun daki wasu kaya da wani jirgin mai saukar angulu ke dauke da su ne jim kadan bayan ya tashi, wanda yayi sanadin fadowarsa kasa inda nan take ya kama da wuta.

Amma daya jirgin ya sami sauka babu wata matsala.

Dukkan jiragen mallakin kamfanin Utair ne wanda kuma na gwamnatin Rasha ne.

Kamfanin dillacin labarai na Rasha TASS ya ruwaito cewa tuni aka dauko bakin akwatin jirgin domin gudanar da cikakken bincike akai.

Labarai masu alaka