Yadda tsoho ke fatan samar da gurji mafi tsawo a duniya

Raghbir Singh Sanghera
Image caption Masana sun ce Kokumbar 'yar asalin Armenia ce tsohon ya shuka

Wani dattijo a Derby ya ce addu'ar da yake wa gurjinsa ya taimaka ta yi girman da za ta kasance mafi girma a duniya.

Raghbir Singh Sanghera, wanda manomi ne a India kafin ya zo Birtaniya a 1991, ya shuka gurjin ne a lambunsa.

Kuma tsawon gurjin yanzu ya kai ma'aunin sentimita 129.54.

Mista Sanghera ya ce gurjin da har yanzu ba a tantance asalinsa ba, yana ci gaba da girma.

Kuma yanzu ya kere gurjin da aka shuka a Wales a 2011 mafi tsawo a duniya a kundin tarihin kamfanin Guinness inda tsawonta ya kai ma'aunin sentimita 107.

Wani masanin shuka kayan lambu ya ce gurjin tsohon dab asalin Armenia ne, wanda yake da bambanci da yanayin nau'in gurjin da aka saba gani.

"Mun taba ganin irin wannan dogon gurjin a wani bikin nuna kayan lambu, amma ba a ba shi muhimmaci ba," in ji Mista Glazebrook

Ya ce akwai nau'insu da ke yin tsawo kuma wadanda za su iya shiga kundin tarihi a duniya.

Kamfanin Guinness ya ba tsohon damar yin takara da gurjin domin shiga kundin tarihi a duniya.

Kakakin kamfanin ya ce ba ya da wani bayani kan wani da ya taba shuka irin wannan dogon gurjin a Armenia.

Image caption Tsawon kokumbar ya sentimita 129.54cm, mafi tsawo a duniya

Mista Sangera ya ce zai dauki gurjin idan ya nuna zuwa wuwin da mabiya addinin Singh ke ibada inda yake aiki a Nottingham domin raba wa mutane.

Ya ce bayan ya cire shi zai kuma ajiye irinta domin sake shuka wa a badi.

Image caption Lambun Mista Sanghera

Labarai masu alaka