Venezuela: Maduro ya tsallake rijiya da baya

Maduro Hakkin mallakar hoto Getty Images

Hukumomin Venezuela sun ce jirage marasa matuka sun sako ababen fashewa a kusa da shugaba Nicolas Maduro a lokacin da yake gabatar da jawabi.

Lamarin ya faru ne lokacin da ake gudanar da bikin sojin kasar da gidan talabijin din kasar ke yadawa kai tsaye a Caracas fadar gwamnatin kasar.

An ga shugaba Maduro ya dakatar da jawabin da ya ke yi tare da kallon sama bayan ya fashewar ta razana shi.

Gwamnatin kasar ya ce jirage marasa matuka biyu ne suka saki ababen fashewa a kusa da shugaban.

Tun da farko an nuna sojojin da ke fareti suna gudu kafin a katse jawabin na shugaba Maduro wanda ake nuna wa kai tsaye a talabijin.

Daga baya shugaban ya fito ya shaida wa 'yan kasar cewa yana raye kuma ba abin da ya same shi.

Sai dai ya zargi Colombia da kuma 'yan adawa, yana mai cewa makiyansa na gida da waje ne suka yi yunkurin halaka shi, zargin da gwamnatin Colombia ta musanta.

Hukumomin kasar sun ce sojoji bakwai suka ji rauni, sannan an kame mutane da dama da ake zargi.

Labarai masu alaka