An yi gargadi ga 'yan Nijar kan siyasar Najeriya
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

An yi gargadi ga 'yan Nijar kan siyasar Najeriya

Kungiyar 'yan Nijar mazauna Najeriya ta gudanar da wani taron fadakar da al'ummarta kan muhimmancin bin doka da oda a daidai lokacin da gangar siyasa ta fara kadawa a Najeriya.

Sai dai mahalarta taron sun koka kan yadda jami'an shige da fice na Najeriya ke gallaza masu kan iyakokin kasashen biyu, duk da tsarin kungiyar ECOWAS ya ba su damar shiga kasashen yammacin Afirka.

Amma Shugaban hukumar shige da ficen na Najeriya Mohamed Baban Deedee ya mayar da martani kan korafin na 'yan Nijar.

Abdou Halilou wanda ya halarci taron ya aiko da rahoto.