Gagarumar girgizar kasa ta auku a tsibirin Lombok na Indonisiya

Map of Indonesia showing location of Lombok and Jakarta

Wata gagarumar girgizar kasa mai karfin lamba 7 a ma'unin Richter ta auku a tsibirin Lombok na Indonisiya.

Lamarin ya sa hukumomi sun sanar da yiwuwar aukuwar igiyar ruwan teku mai karfi ta tsunami a yankin.

Hukuma mai kula da girgizar kasa ta Amurka, US Geological Survey, ta ce girgizar ta auku ne arewa da tsibirin, kilomita 10 a karkashin kasa.

Tsibirin Lombok wata cibiya ce ta masu yawon bude idanu, kuma yana da nisan kilomita 40 ne gabas da Bali.

Kawo yanzu ba a sami bayanin wadanda suka jikkata ko suka rasa rayukansu ba, amma jami'ai sun yi gargadin aukuwar igiyar ruwa ta tsunami, kuma sun shawarci jama'a da suk janye daga yankunan da ke kusa da gabar teku.

Mazauna Bali sun ji wannan girgizar kasar na kusan minti guda, lamarin da yasa su ka yi ta ficewa daga cikin gidajensu.

Labarai masu alaka