Hanyoyi biyar na yaki da shan miyagun kwayoyi

Bayanan bidiyo,

Kalli bidiyon yadda matasa ke rububin shan Codeine

Wani bincike da BBC ta gudanar kan sayar da magungunan rage radadin ciwo ba a bisa ka'ida ba ya janyo sauye-sauye a Najeriya da makwabtan kasashe.

Cikin sa'o'i 24 da yada binciken sashen musamman na Africa Eye, wanda ya bankado yadda mutane a wasu manyan kamfanonin sarrafa magunguna a Najeriya ke siyar da magungunan tari masu dauke da sinadarin Codeine daga kamfanonin zuwa masu sayar da magunguna, aka haramta sayar da maganin.

Ga wasu abubuwan da suka faru tun bayan yada shirin talabijin na musamman mai suna Sweet Sweet Codeine a watan Mayu.

1. An mayar da miliyoyin kwalabe kamfani

Fiye da kwalaben maganin tari mai dauke da sinadarin Codeine miliyan 2.4 ne gwamnatin kasar ta mayar kamfani daga kasuwa.

Bayanan hoto,

Jami'an yaki da sha da kuma fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya na duba wani maganin tarin mai dauke da Codeine da aka kwace a Kano

Wannan babbar nasara ce ga masu yaki da shan miyagun kwayoyi kuma babbar asarar kudi ga kamfanonin sarrafa magunguna, wadanda a da suke siyar da kwalbar magani guda har naira dubu uku wato dala takwas ko kuma fan shida.

A baya gwamnati ta yi kiyasin cewa a na shanye sama da kwalaben maganin tari mai dauke da Codeine miliyan uku, wanda kuma ke haifar da lalacewar kayan ciki idan aka fiye amfani da shi, kulli yaumin a jihohi biyu.

Da zarar an kammala mayar da kwalaben, gwamnatin Najeriya za ta tattara tarin miyagun kwayoyin da kudinsu zai kai miliyoyin fama-famai.

Har yanzu dai ba a san yadda za su zubar da shi ba, duk da dai an kona maganin da yawa da aka kwato daga kasuwar bayan fage.

2. Kamamasu tserewa

An kama gwamman mutane tun bayan da gwamnatin Najeriya ta haramta amfani da maganin tari mai dauke da Codeine da yawansu masu sarrafa magunguna ne da kuma kananan 'yan kasuwa.

A wani farmaki da a ka kai a jihar Kwara, wanda babban jigo ne binciken na BBC, mutane 17 aka kama suna kokarin fasa kwaurin kwalaben maganin a Kaduna. A wasu jerin farmaki da aka kai a Katsina, daliban jami'a 21 ne aka kama da kwalabe 128 na Codein.

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya, NDLEA ta karkatar da kayan aiki zuwa iyakar Kamaru domin hana mutane fasa kwaurin kodin zuwa kasashen waje.

Bayanan hoto,

Chukwunonye Madubuike, tsohon ma'aikacin kamfanin sarrafa magunguna na Emzor ya tsere

An bayar da odar kama Chukwunonye Madubuike, tsohon mai kula da ci gaban kasuwanci a kamfanin sarrafa magunguna na Emzor wanda aka tona wa asiri a binciken BBC amma har yanzu ba a san inda ya ke ba. Amma kamfanin Emzor ya kore shi daga aiki.

3. Haramtawa a Ghana

Shirirn na musamman na yin tasiri a sauran kasashen Afirka.

Jim kadan bayan da BBC ta bankado kasuwar bayan fagen siyar da magungunan Codeine da kamfanonin sarrafa magunguna a Najeriya, hukumar sarrafa magunguna ta Ghana ta kaddamar da wani bincike kan amfani da Codeine ba a bisa ka'ida ba, har ma da wani maganin kashe radadin ciwon, Tramadol.

Bayanan hoto,

An kai farmaki otel-otel a Najeriya inda aka kwace kwalaben magungunan tari

Binciken ya yi bitar shagon saida magunguna 35 kuma ya gano cewa ana shan magungunan a birnin Kumasi.

A watan Yunin shekarar 2018, cikin wani shiri da kasar ta shirya na bitar manufofin magunguna, Ministn Lafiya Kwaku Agyeman-Manu ya sanar da cewa za a haramta samarwa da shigar da kodin daga Ghana.

4.Nunawa a bainar jama'a

Jama'ar gari da kungiyoyi masu zaman kansu na ci gaba da nuna bidiyon Sweet Sweet Codeine a fadin Najeriya, inda yake janyo hankulan jama'a.

Wani rahoto na majalisar dattawan Najeriya ya ce ana shan miyagun kwayoyi ya fi shafar mata matasa.

A arewacin Najeriya inda mafi rinjaye Musulmi ne, an haramta shan giya kuma maganin tari ya zamo abin mayen da ake tu'ammali da shi.

Fiye da mata 2,000 sun halarci taron nuna shirin na musamman a Keffi, arewacin Najeriya a watan Yuni.

A lokacin wani taron nuna shirin a Kaduna a ranar 29 ga watan Yuli, sama da daliban jami'a 4,000 ne suka taru domin kallon shirin kuma suka tafka muhawara kan yadda za a magance matsalar shaye-shayen kwayoyi.

Mairo Mandara, tsohuwar wakiliyar gidauniyar Bill and Melinda Gates Foundation, ta shirya irin wadannan tarukan a lokuta da dama kuma tana jagorantar yaki da kawo karshen shan Codeine a kasar.

Bayanan hoto,

Masu fafautuka na so su zaburar da mata matasa ga hadarin maganin tari

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Ta ce binciken Africa Eye ya taka muhimmiyar rawa wajen zaburar da kasar kan yaki da magungunan rage radadin ciwo.

"Sweet Sweet Codeine ya kasance kololuwa a kamfe din mu na haramta shan maganin tari mai Codeine a Najeriya," kamar yadda ta ce.

"Tun da aka haramta shan maganin, akalla mata da yara mata da maza sun kira ni su a neman taimako.

"Har yanzu mu na nuna shirin a fadin kasar a makarantu da masallatai da coci-coci da sansanin masu yi wa kasa hidima."

5. Hukunci

Lokacin da gwamnatin Najeriya ta fara haramta shan maganin Codeine a watan Mayu, an yi shi ne ta hanyar umarnin ma'aikatar lafiya.

Zuwa karshen watan Mayu, majalisar wakilai ta yi daftarin tsauraran dokoki da su ka shafi nacewa Codeine da Tramadol.

A baya, wadanda aka kama da Codeine ko Tramadol ba sa fuskantar hukunci.

Yanzu, ana iya kai mutum kurkuku tsawon shekaru biyu kuma a ci tarra shi fiye da naira miliyan daya idan aka kama shi da kwayoyin ko kuma abin da ya danganci haka.

Bayanan hoto,

Mayakan Boko Haram sun yi kaurin suna wajen safarar Tramadol

Ba kamar maganin tari mai dauke da kodin ba, wanda ake sarrafa shi a kasar, Tramadol shigo da shi a ke yi kuma akwai tsoron cewa magungunan rage radadin ciwo na rura wutar Boko Haram a Arewa maso gabashin kasar.

A cewar hukumar yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi ta Najeriya, kashi 20 cikin 100 na Tramadol da ake safarar shi ba a bisa ka'ida ba a duniya an kwace shi ne a Najeriya a bara.

A wani bincike da aka gudanar a filin jirgin sama na Legas a watan Mayu, fiye da kilogram 4,000 na Tramadol aka kwace.