An kama wani jigo a kungiyar Boko Haram

Boko Haram

Asalin hoton, Getty Images

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta cafke Maje Lawan ne a wani sansanin 'yan gudun hijira da ke garin Banki a jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar.

Hakan yana kunshe ne a wata sanarwa da rundunar ta fitar mai dauke da sa hannun daraktar yada labaranta, Birgediya Janar Texas Chuku, inda ta kara da cewa an kama mutumin da ake zargin ne a ranar Asabar.

Mutumin shi ne mutum na 96 a cikin jerin sunayen 'yan Boko Haram 100 da rundunar sojin kasar take nema ruwa a jallo.

Kawo yanzu dai yana ci gaba da kasancewa a hannun sojoji zuwa lokacin da za a kammala bincike a kan lamarin.

Sai dai rundunar ba ta ya yi wani karin bayani ba kan yadda aka yi dan Boko Haram din da ake zargi ya kasance a sansanin da kuma tsawon lokacin da ya kwashe a can, duk da matakan tantance mutane da hukumomi ke cewa suna dauka don tabbatar da cewa hakan bai faru ba.

Kodayake a baya rundunar ta sanar da kama kalilan daga cikin 'yan kungiyar ta da ta ce tana nema ruwa a jallo, amma kama Maje Lawal ya kara sanya alamar tambaya a kan matakan tattara bayanan sirri da hukumomin tsaron kasar ke cewa suna amfani da shi.

A baya dai an sha kai hare-haren kunar bakin wake a wasu sansanonin 'yan gudun hijirar da ke yankin na arewa maso gabashin kasar.