Saraki zai yi zaman gaggawa da shugabannin majalisa

Saraki da Dogara

Asalin hoton, Twitter/The Senate

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Bukola Saraki zai yi zaman gaggawa da sauran shugabannin majalisar dokokin kasar a ofishinsa da ke Abuja ranar Talata.

Wani na kusa da shugaban majalisar wanda ya bukaci a sakaya sunansa ne ya shaida wa BBC hakan.

Ya ce za a yi zaman ne tsakanin shugabannin majalisar dattawan da na wakilai kuma za su kwashe tsawon sa'a guda suna tattaunawar.

Ya ce cikin batutuwan da za su tattauna har da batun zaben shekarar 2019, da batun sauya shekar wasu 'yan majalisar kasar.

Sai dai sabanin yadda wasu rahotanni suka bayyana, zaman ba zai duba batun tsige Sanata Saraki daga shugabancin majalisar ba.

"Wannan ba ya daga cikin batutuwan da za su tattauna," a cewarsa majiyar BBC.

A karshen watan jiya ne majalisar ta tafi dogon hutu bayan sauya shekar wasu 'yan majalisa fiye da 50 daga jam'iyyar APC mai mulki zuwa PDP.

Akwai wasu rahotanni wadanda ba a tabbatar ba da ke cewa akwai wani shirin tsige Sanata Saraki daga kujerarsa, bayan da shi ma ya sauya sheka daga APC zuwa PDP a makon jiya.

Jerin sunayen jiga-jigan da suka sauya sheka daga APC zuwa yanzu

Asalin hoton, .

Bayanan hoto,

Wadannan na cikin 'yan majalisar dattawan da suka sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa PDP

Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki

Gwamnan jihar Sokoto Aminu Tambuwal

Kakakin jam'iyyar APC Bolaji Abdullahi Ahmed

Jakadan Najeriya a Afirka Ta Kudu, Ahmed Ibeto

Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom

'Yan majalisar dokoki ta kasa fiye da 50 sun sauya sheka daga APC zuwa PDP da suka hada da Kwankwaso da Hunkuyi da Melaye da Hamma Misau da Nazif Gamawa da sauran su

Bangaren Akida da Restoration a jihar Kaduna wadanda ke rigima da Gwamna Nasir el-Rufa'i

Bangaren rAPC na Buba Galadima ya kulla alaka da PDP domin kayar da APC a 2019 - wasu na ganin su ma sun kama hanyar ficewa daga jam'iyyar

Sanata Abdul-Azeez Nyako da Dan majalisar Wakilai Rufai Umar daga Adamawa sun koma jam'iyyar ADC

Hakeem Baba Ahmed - shugaban ma'aikata a ofishin Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki

Usman Bawa - mataimaki na musamman ga Kakakin Majalisar Wakilai Yakubu Dogara.