'Yan kunar bakin wake biyar sun kashe kansu a Maiduguri

Mahara biyar ne su ka kai harin

Asalin hoton, BOUREIMA HAMA

Bayanan hoto,

Mahara biyar ne su ka kai harin a unguwar Kaleri

Wasu da a ke zargin 'yan kunar waken kungiyar Boko Haram ne sun kai hari a maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Babban jami'in hukumar agaji ta gaggawa mai kula da Arewa maso Gabashin Najeriya, Bashir Garga ya shaida wa BBC cewar harin ya faru ne da misalin karfe 10 na daren Lahadi a unguwar Kaleri da ke cikin birnin Maiduguri.

Mazauna yankin sun ce sun ji karar fashewar bama-baman cikin dare.

Mahara biyar ne su ka kai harin inda guda uku mata ne, guda biyu kuma maza - dattijo daya da matashi daya.

Gaba daya maharan sun mutu, yayin da wasu mutum uku su ka samu raunuka, inda a yanzu su ke asibiti inda a ke basu kulawa.

Har yanzu dai babu wanda ya fito ya dauki alhakin kai harin, amma kungiyar Boko Haram ce aka sani da yawan kai hare-hare wannan yankin.

Wannan ne dai hari na farko cikin kusan wata biyu a birnin na Maiduguri.

Har yanzu kungiyar Boko Haram na kai hare-hare kan fararen hula da jami'an tsaro, duk da ikirarin da gwamnatin Najeriya ke yi cewa ta "murkushe" su.

A mako biyu da suka gabata maharan da ake zargi 'yan kungiyar ne sun kai wa sojoji hari, inda rahotanni suka ce an kashe sojoji da dama tare da kwace makamai, sakamakon kwanton baunar da suka yi wa dakarun tsaron.

Hukumomi sun cean kashe 'yan Boko Haram da dama a wannan arangamar.

Rundunar sojin Najeriyar dai ta sauya kwamandan da ke jagorantar rundunar da ke yaki da kungiyar bayan wannan artabun.

Karin Labaran da za ku so ku karanta