Jami'an tsaro sun hana Sanatoci shiga majalisa

ile asofin Hakkin mallakar hoto @lorghenkwange
Image caption 'Yan majalisar dattawan Najeriyar dai suna son gudanar da wani taron gaggawa ne

Jami'an tsaron Najeriya na farin kaya (DSS) sun hana wasu 'yan majalisar dattawan kasar shiga zauren majalisar da safiyar Talata.

Jami'an, da suka ce sun tare hanyar shiga zauren ne bisa umarnin da aka ba su 'daga sama', sun kyale 'yan majalisar sun shiga zauren majalisar daga baya.

Rahotanni dai suna zargin cewar hana 'yan majalisar shiga na da alaka da yunkurin tsige shugaban majalisar, Bukola Saraki.

Wannan lamarin ya auku ne a lokacin da ake ci-gaba da takun-saka tsakanin shugaban majalisar da wadanda ke son tsige shi.

Wasu 'yan majalisar dake jam'iyyar APC suna ganin ya kamata Saraki ya yi murabus daga mukaminsa tun da dai ya fice daga jam'iyyar APC mai mulki.

Sai dai kuma wasu 'yan jam'iyyar PDP suna ganin bai kamata Saraki ya sauka daga mukaminsa ba.

A ranar Litinin ne Shugaban Majalisar Dattawan Najeriyar Bukola Saraki ya sanar da cewa zai yi zaman gaggawa da sauran shugabannin majalisar dokokin kasar a ofishinsa da ke Abuja ranar Talata.

Wani na kusa da shugaban majalisar wanda ya bukaci a sakaya sunansa ne ya shaida wa BBC hakan.

Ya ce za a yi zaman ne tsakanin shugabannin majalisar dattawan da na wakilai kuma za su kwashe tsawon sa'a guda suna tattaunawar.

Ya ce cikin batutuwan da za su tattauna har da batun zaben shekarar 2019, da batun sauya shekar wasu 'yan majalisar kasar.

Hakkin mallakar hoto Bukola Saraki/Facebook
Image caption Rahotanni sun ce cikin 'yan kwanakinnan an yi ta matsa wa Bukola Saraki ya kira zaman majalisar na gaggawa

Sai dai sabanin yadda wasu rahotanni suka bayyana, zaman ba zai duba batun tsige Sanata Saraki daga shugabancin majalisar ba.

"Wannan ba ya daga cikin batutuwan da za su tattauna," a cewarsa majiyar BBC.

A karshen watan jiya ne majalisar ta tafi dogon hutu bayan sauya shekar wasu 'yan majalisa fiye da 50 daga jam'iyyar APC mai mulki zuwa PDP.

Jerin sunayen jiga-jigan da suka sauya sheka daga APC zuwa yanzu

 • Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki
 • Gwamnan jihar Sokoto Aminu Tambuwal
 • Kakakin jam'iyyar APC Bolaji Abdullahi Ahmed
 • Jakadan Najeriya a Afirka Ta Kudu, Ahmed Ibeto
 • Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom
 • 'Yan majalisar dokoki ta kasa fiye da 50 sun sauya sheka daga APC zuwa PDP da suka hada da Kwankwaso da Hunkuyi da Melaye da Hamma Misau da Nazif Gamawa da sauran su
 • Bangaren Akida da Restoration a jihar Kaduna wadanda ke rigima da Gwamna Nasir el-Rufa'i
 • Bangaren rAPC na Buba Galadima ya kulla alaka da PDP domin kayar da APC a 2019 - wasu na ganin su ma sun kama hanyar ficewa daga jam'iyyar
 • Sanata Abdul-Azeez Nyako da Dan majalisar Wakilai Rufai Umar daga Adamawa sun koma jam'iyyar ADC
 • Hakeem Baba Ahmed - shugaban ma'aikata a ofishin Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki
 • Usman Bawa - mataimaki na musamman ga Kakakin Majalisar Wakilai Yakubu Dogara.

Labarai masu alaka