Burnley ta sayi golan Manchester City a kan fam miliyan 3.5

Golan baije gasar cin kofin duniya da akayi a Rasha ba Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ingila ba ta je da golan gasar cin kofin duniya da aka yi a Rasha ba

Burnley ta sayi golan Manchester City Joe Hart a kwantaragin shekara biyu a kan fam miliyan 3.5.

Shugaban kungiyar Sean Dyche ya ce ya sayi golan ne bayan da sauran gololin kungiyar biyu wato Nick Pope da Tom Heaton suka ji rauni.

Hart, wanda ya yi wa kasar Ingila wasanni 75, ya kuma yi wa City wasanni 350, inda suka lashe kofin Firimiya biyu da kuma Kofin FA daya.

Golan ya fara nuna sha'awar barin City ne tun bayan da Kocin Kungiyar Pep Guardiola ya rika ajiye shi a benci.

Sau daya Hart ya kama wa City gola tun bayan da Guardiola ya zama kocin kungiyar a shekarar 2016.

Ya kuma kwashe kaka biyu a matsayin aro a kungiyar Torino da kuma West Ham.

Hakazalika kasar Ingila ba ta je da shi gasar cin kofin duniya da aka yi a kasar Rasha a shekarar 2018.

Labarai masu alaka

Labaran BBC

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba