'Buhari bai ce a tsige Saraki ba'
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

'Buhari bai ce a tsige Saraki ba'

Fadar gwamnatin Najeriya ta nesanta kanta daga matakin da jami'an tsaron farin kaya wato DSS suka yi na datse babbar kofar shiga majalisar dokokin kasar.

Mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan ayyukan Majalisar wakilai, Abdurrahman Kawu Sumaila ya musanta cewa bangaren zartarwa na da hannu a wani yunkuri da ake ta yadawa na kokarin tsige shugaban Majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki daga kan mukamin sa.

Ya ce matakin da mukaddashin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya dauka na korar shugaban DSS Lawal Daura, na nuna cewa matakin da jami'an tsaron suka dauka na hana sanatoci shiga majalisar, gaban kansu suka yi.