Saudiyya ta kirkiro manhajar kimanta wa'azi

Wani mutum na karanta Al Kur'ani mai girma a masallaci a Saudiyya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hukumomin Saudiyya na ciyar da Musulunci mai sassauci gaba

Hukumomi a Saudiyya na kirkirar wata manhajar wayar hannu wacce za ta sa ido kan wa'azuzzuka da addu'o'i a masallatai domin bai wa masu ibada damar sani idan mai wa'azi zai dade yana wa'azin.

Jaridar Al-Watan ta kasar Saudiyya ta ruwaito cewa Ministan harkokin musulunci na kasar Abdul Latif Al-Sheikh, ya bayyana cewa manhajar za ta bayar da damar sa ido a masallatai, kan tsawon lokaci da kuma ingancin wa'azuzzukan duk minti kuma duk dakika.

Ba a bayyana wanda zai rika sa idon ba, amma a na tunanin masu zuwa masallaci ko da yaushe za su iya kimanta mai wa'azin a wasu bangarori a harkar aikinsu.

A halin da a ke ciki, Saudiyya na duba batun kawo sauyi a koyarwar addini, kuma a na ci gaba da muhawara kan daidaita abubuwan da a ke wa'azi a kan su domin karakatar da mutane daga ra'ayin kasashen waje, ko na bangaranci ko kuma na kungiyar 'yan uwa musulmi.

Ministan ya ce addini "ba fagen da za a rikita zukatan mutane ba ne, ko kuma a yi sagegeduwa da tsaro da zaman lafiyar kasar nan mai albarka ba".

A shekarar 2014 ne hukumomin Saudiyya suka ayyana Kungiyar 'yan uwa musulmi a matsayin kungiyar 'yan ta'adda.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Yanzu 'yan Saudiyya na iya kimanta ayyukan gwamnati a wayoyinsu na hannu

Don gina al'umma mai sassaucin ra'ayi

Jaridar intanet ta Sabq ta ruwaito cewar manhajar kimanta wa'azin ta zo ne 'yan kwanaki bayan kaddamar da wata manhajar wayar hannu inda 'yan kasar Saudiyya za su iya kimanta ko wani irin aikin gwamnati, daga kiwon lafiya zuwa wasanni da walwala.

An yi wa manhajar ta Watani lakabi da "manhajar wayar hannu da zata bai wa 'yan kasar da mazauna kasar da baki damar kimanta ayyukan gwamnati, sannan su kimanta gamsuwarsu kuma su bayar da gudummawa ga kokarin da a ke yi na inganta ayyukan gwamnati".

Da alama yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman ne ke jagorantar sauye-sauyen da a ke yi a Saudiyya yanzu, wanda shirinsa na kawo sauyi a masarautar ya hada da dawo da "sassauci a addinin musulunci" da kuma al'umma.

Sai dai kuma, a wannan makon Saudiyyar ta ce za ta kori Jakadan Kanada kuma za ta dakatar da kawancen kasuwanci bayan da Kanadar ta bukaci a saki masu fafutukar kare hakkin dan adam a masarautar.

Abdirahim Saeed da Alistair Coleman su ka hada wannan rahoton.

Labarai masu alaka