'Yadda 'yan fashi suka kora mu cikin daji kamar shanu'

'Yan bindiga sun sha kai hari a kauyukan Zamfara Hakkin mallakar hoto Getty Images

Wani da 'yan fashi suka sace a Najeriya ya zanta da BBC, inda ya bayyana yadda aka tare su a kan hanya sannan aka kora su cikin daji bayan an yi masu fashi.

Mutumin wanda aka tare shi yayin da yake ka hanyarsa ta zuwa Gusau ya ce 'yan fashin na amfani da wasu sautuka domin sadarwa a tsakanin su.

"Zan je Gusau, ina kan hanya kafin na kai Giwa, sai na ga mutane da kayan sojoji."

"Sai muka ji an bude wuta ana ta harbi."

"Suna cewa tsaya ko in harbe ka."

A cewar mutumin, an tare motoci da dama a lokacin fashin, sannan an kwace masu kudade da wayoyinsu na hannu.

"Bayan an gama fashin sai suka kora mu cikin daji suna dukan mu."

Ya tabbatar da cewa an kwashe kimanin minti talatin ana fashin ba tare da jami'an tsaro sun kawo dauki ba.

Latsa alamar lasifikar da ke kasa don sauraron cikakkiyar hirar da BBC ta yi da mutumin:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Hira da wanda barayi suka sace

Labarai masu alaka