Kun san wanda ya rasa ransa wajen ceto mutane a kogi a Fatakwal?

Joe Blankson and im wife Mercy plus dia son Owen wen im be two years old. Hakkin mallakar hoto FACEBOOK/JOE BLANKSON
Image caption Joe Blankson and im wife Mercy plus dia son Owen wen im be two years old.

Mercy, matar marigayi Joe Blankson wanda ya rasa ransa bayan da ya ceto mutum 13 daga kogi, ta ce har yanzu tana ganin mutuwar mijin nata tamkar mafarki, kwana tara bayan jana'izarsa.

Mr Blankson ya samu yabo ta ko ina inda aka mayar da shi gwarzo sakamakon rasa ransa da ya yi a garin ceto mutane bayan da jirgin ruwan da suke ciki ya kife a kogi a jihar Fatakwal.

Mista Blankson ne kadai wanda ya rasa ransa a hatsarin jirgin ruwan da ya faru ranar Asabar 28 ga watan Yulin.

Matarsa Mercy ta shaida wa sashen Turancin Buroka na BBC cewa abin da mijinta ya yi bai ba ta mamaki ba, saboda ta san shi wajen son taimakon mutane.

"Mijina yana da kirki sosai... ya fi damuwa da taimakon wasu kafin kansa. Idan da zai ji ihun wani da karfe biyar na asuba, to zai iya fita shi kadai don ganin me yake faruwa," in ji ta.

Ta ce ko a hanya Mista Blankson ya ga ana fada to yana iya tsayar da motarsa don ya je ya raba.

Blankson, mai shekara 38, ya auri Mercy shekara biyar da ta gabata, kuma suna da 'ya'ya uku, amma babbar 'yarsu ta rasu a watan Disambar 2016.

Hakkin mallakar hoto Mercy Blankson/Facebook
Image caption Mercy ta ce ta ga wasu alamu kafin mutuwar tasa

Mercy ta ce har yanzu ta kasa yarda cewa mijinta ya mutu saboda a wasu lokutan, sai ta ga kamar zai koma gida.

"Gidan babu dadi sam da baya nan," in ji ta.

"Rannan ma haka dana Owen ya dauki jakarsa ya ce zai tafi Bakana neman babansa."

Yadda mummunan labarin ya iske ta

A wannan bakar rana ta Asabar 28 ga watan Yulin 2018, yayin da Joe ya tafi aiki, ya shaida mata cewa daga wajen aiki zai wuce Bakan don halartar wata jana'iza.

Amma yayin da ta ga dare yana kara yi kuma Joe bai kirata ba kamar yadda ya saba, sai ta yi ta kiran wayarsa, amma sai ta ji ta a kashe.

Sai Mercy ta yi ta kiran abokan Joe amma dukkansu ba wanda ya iya gaya mata komai. Daga nan sai ta shiga damuwa.

Daga baya ne sai mahaifiyar Joe ta kirata ta shaida mata cewa kwale-kwale ya kife a Bakana kuma mijinta na ciki don haka sun tafi nemansa.

Sai ta ce mata tana fatan su same shi a raye. Sai ta tafi gidan surukarta inda ta iske dafifin mutane suna ta kuka, kuma suka ce mata ai ba a gan shi ba.

Hakkin mallakar hoto Mercy Blankson/Facebook

Sai washegari ranar Litinin 30 ga watan Yuli ne sai matar wan mijinta ta shaida mata cewa ai Joe ya mutu bayan da wani masunci ya gano gawarsa na yawo a saman kogi.

Daga nan fa sai ta fara kuka.

Sai ta ruga zuwa bakin kogin Abonnema amma sai aka hana ta ganin gawarsa saboda tana shayarwa, kuma a bisa al'ada duk mutumin da ya mutu a cikin ruwa, to a ruwa ake binne shi.

Don haka ba ta san inda suka binne mijinta ba.

Mercy ta ce ta ga wasu alamu kafin mutuwar tasa.

Ta ce mako guda kafin mutuwar Joe, sun je wani waje don halartar liyafar murnar zagayowar ranar haihuwar makwabtansu.

Sai ta ce masa karo na karshe da ta zo wannan waje, washe gari aka yi wata gobara da ta yi sanadin mutuwar 'yarsu ta fari, don haka jikinta na ba ta wani mummunan abu zai faru nan ba da jimawa ba.

Amma sai mijinta ya ce ta kwantar da hankalinta ba abin da zai faru. A wannan Asabar din kuwa sai Joe ya mutu.

Rayuwa bayan mutuwar Joe

Mercy ta ce tana fatan mutuwar Joe za ta sa gwamnati ta yi wani abu don kawo gyara a kogin Abonnema, don samar da kwararrun masu iyo da rigunan ruwa ga dukkan fasinjojin da ke hawa kwale-kwale.

Ta ce ya kamata a samu 'yan sandan bakin ruwa da za su dinga lura da al'amuran zirga-zirga a kogin da kuma tsaftace kogin, ta yadda datti ba zai dinga makalewa a injinan kwale-kwalen ba da har zai jawo hatsari.

A yadda al'amura suke tafiya yanzu, Mercy ta ce gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike, ya yi alkawarin tallafa wa karatun yaranta da kuma ba ta aikin gwamnati a jihar.

Ta ce yana da kyau a gina wani abu a Bakana don tunawa da mijinta wanda ya mutu saboda nan gaba idan yaranta suka tambaye ta inda aka binne babansu, sai ta nuna musu wannan gini a matsayin nan ne kushewar mahaifinsu.

Labarai masu alaka