Hukumar EFCC za ta 'binciki' Lawal Daura

EFCC Nigeria Hakkin mallakar hoto Getty Images

Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta'annati za ta binciki tsohon shugaban hukumar tsaro ta farin kaya DSS, Lawan Daura, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Batutuwan da za a masa tambayoyi a kai sun shafi yadda hukumar da ya jagoranta ta kashe naira biliyan 17 da ya gada daga tsohon shugaban hukumar Mista Ita Ekpeyong, a cewar rahotannin.

Ana kuma zargin Mista Ekpeyong da ya karbi Naira biliyan 20 daga babban bankin Najeriya a karshen mulkin gwamnatin Shugaba Goodluck Jonathan.

Rahotannin suna cewa Mista Ekpeyong ya canza Naira biliyan 17 zuwa dalar Amurka wanda ya bari a baitumalin hukumar lokacin da ya mika ragamar shugabanci ga Lawal Daura.

Har ila yau rahotannin sun ce jami'an hukumar EFFC sun bankado batun kudin ne bayan makudan kudin da suka kai dala miliyan 43 da aka gano a wani gida da ke Legas wanda ke da alaka da hukumar tattara bayanan sirri ta kasa, NIA.

Jami'an hukumar ta EFFC sun rika kokarin gudanar da bincike kan yadda hukumar DSS ta kashe kudin, sai dai sun yi zargin cewa tsohon shugaban hukumar da mukaddashin shugaban kasa ya sallama ya rika kawo cikas.

Jami'an hukumar EFFC sun yi zargin cewa Lawal Daura ya hana jami'an nasu kama tsohon shugaban hukumar DSS Ita Ekpeyong da kuma tsohon shugaban hukumar tattara bayanan sirri ta kasa Ayo Oke a samamen da suka kai a ranar 21 ga watan Nuwambar shekarar 2017.

BBC ta yi kokarin jin ta bakin kakakin hukumar EFCC Wilson Uwajeren a kan lamarin, sai dai hakan bai cimma ruwa ba, domin an ce ba ya ofis.

Sai dai ya zuwa lokacin aka hada wannan rahoton, hukumar EFCCn ba ta musunta rahotannin ba.

A hukumance dai ba a bayyana wurin da ake tsare da tsohon shugaban hukumar ta DSS ba.

Kodayake rahotannin sun ce ana tsare da shi ne a sashin yaki da miyagun laifuka na hukumar 'yan sanda.

Sai dai kakakin hukumar 'yan sanda Jimoh Moshood ya shaida wa BBC cewa ba shi da masaniya game da wurin da ake tsare da shi.

A ranar Litinin ne mukadashin shugban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya kori Malam Lawal Daura daga aiki sakamakon jami'an tsaron farin kaya da aka tura zuwa Majalisar Dokokin kasar ba tare da sannin fadar shugaban kasa ba.

Labarai masu alaka