Abin da ya faru a Afirka makon jiya

Zababbun hotuna masu kayatarwa daga sassa daban-daban na Afirka da aka dauka a makon jiya.

Dubban 'yan addinin Ethopia sun taru a Millenium hall a Addis Ababa ranar asabar. Tens of thousands of Ethiopian Orthodox believers gather at Millennium Hall in Addis Ababa - 4 August 2018

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wannan matar na daya daga cikin Kristoci 10 na Ethopia da suke murnar dawowar Bishof Merkorios da aka kora daga birnin Addis Ababa a ranar Juma'a.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Yaran da ba a haifa ba a lokacin da bishof din ya gudu Amurka shekara 27 da ta wuce suma sun shiga jerin wadanda ke wakokin addini a babban dakin Millenium.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Ranar Talata: Dakaru na musamman na Ivory Coast sun shafa ma fuskokinsu launin tutar kasarsu, a lokacin wani fareti na murnar cika shekara 58 da samun 'yancin kai daga kasar Faransa.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wani mutum ya halarci wani taron jin ra'ayin jama'a kan shirin da gwamnatin ke yi na karbe filayen fararen fata ba tare da biyan diyya ba a yankin Cape Town na Afirka ta Kudu.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

A ranar Asabar mutane sun fito da motoci masu kama da wadanda 'yan sanda suka yi amfani da su a wurin kama Nelson Mandela shekaru 56 da suka gabata.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Ranar Asabar wani dalibi mai karantun kimiyya da fasaha na tuka motarsa mai amfani da iskar gas da ya kirkiro domin tsaftace iska a babban birnin Masar, al Kahira

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

A ranar Litinin wani mutum a birnin al Kahira ya wuce ta gaban wani allo da aka rubuta "Masar na zukatanmu."

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

A ranar Litinin din dai, wata yarinya a Zimbabwe ta tsaya kusa da wani hoton shugaban kasar Emmerson Mnangagwa da aka lalata a Harare babban birnin kasar.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Su kuma wadannan 'yan matan sun je makarantar Lahadi-Lahadi ce ta cocin Katolika na birnin Harare ranar Lahadin da ta gabata.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Wata mata da ta rasa dangi a wani harin bom da kungiyar al-Qaeda ta kai a babban birnin kasar Kenya shekaru 20 da suka gabata. Fiye da mutane 200 ne suka mutu a harin.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

A ranar Alhamis kuwa a kasar Masar, wasu maza ne suka dauko tunkiya a kan babur a wajen garin Giza wanda ke cikin shirye-shiryen sallah babba.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

A wannan hoton kuma mai sayar da dabbobi ne ke a jan wata tunkiya domin ya kai ta mota, ya saye ta ne domin bikin sallah babba.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

A ranar Talata wani mahayin doki ya nuna kwarewarsa ta sukuwar doki a wani taro na shekara-shekara da aka fi sani da the "Knights of Libya Festival".

Wadannan hotunan an samo su ne daga AFP, EPA, Getty Images da Reuters