Marar lafiya ya lakada wa Likita duka a Jihar Ondo

Marar lafiyan ya far wa likitocin da ma'aikatan jinya har daya daga cikinsu ya suma Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Marar lafiyan ya far wa likitocin da ma'aikatan jinya har daya daga cikinsu ya suma

Wani marar lafiya ya far wa tare da raunata wasu likitoci biyu da kuma ma'aikatan jinya uku a Jihar Ondo da ke kudu maso yammacin Najeriya.

Rahotanni sun ce mara lafiyar mai fama da tabin hankali ya fusata ne lokacin da ma'aikatan jinyar suka zo su ba shi magani.

Ya far wa likitoci biyu da kuma ma'aikatan jinya uku inda ya raunata biyu daga cikinsu kuma ya lakadawa daya daga cikin likitocin duka har sai da ya suma.

Rahotannin sun ce wani da yake jinya a asibitin ne ya kubatar da likitocin biyu daga hannun maralafiyan.

Lamarin ya sa ma'aikatan jinyar dakatar da aikinsu har sai gwamnati ta dauki matakin tabbatar da tsaron lafiyarsu, inda suka yi zanga-zanga rike da kwalaye domin nuna rashin jin dadinsu kan yadda rayuwarsu ke cikin hadari da kuma rashin matakan tabbatar da tsaron lafiyarsu, abinda ya sa ayyuka suka tsaya cak har na wasu yan sa'o'i.

Shugaban kwamitin sulhu na gwamnatin jihar Ondo Opeyemi Oloniyo ya tabbatar wa BBC da aukuwar lamarin kuma ya ce al'amura sun daidaita kuma ma'aikatan jinyar sun koma bakin aiki.

BBC ta tambayi Mr Opeyemi a kan matakin da gwamnat ta dauka game da korafe-korafen ma'aikatan sai ya ce "ba a fafe gora ranar tafiya, a hankali a hankali ake abubuwa.

Ma'aikatan jinya a Najeriya dai sun dade suna korafi game da yanayin da suke aiki, inda a wasu lokutan su kan shiga yajin aiki domin matsawa gwamnati lamba.

Labarai masu alaka