Yadda ake cinikin ragunan Sallah ta Intanet a Aljeriya

Ana sayen miliyoyan raguna da tumaki domin Sallar layya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ana sayen miliyoyan raguna da tumaki domin Sallar layya

Matsalar satar ragunan Sallah ya sa masu sayar ragunan Sallah da tumaki a Aljeriya sun koma suna amfani da shafin Facebook da wasu shafukan intanet domin tallar dabbobinsu.

Suna fatan cinikayya ta hanyar Intanet zai kare su daga hatsarin da ke tattare da daukar dabbobinsu zuwa birane don sayar wa a lokutan sallar layya, saboda an dade ana yi wa 'yan kasuwa duka a kwace dabbobinsu, kamar yadda shafin jaridar intanet na Echourouk ya ruwaito.

Shafin Facebook da Ouedkniss.com a Algeria, ya ba 'yan kasuwa damar saka hotunan dabbobinsu daga gida domin talla.

Sannan akwai wani shafi kuma da ke tallar dakon dabbobin ga 'yan kasuwa zuwa ga wadanda suka saya a Intanet.

'Yan kasuwar yanzu na amfani da shafin Facebook domin tallan ragunan sallah a sassan Aljeriya don gujewa hatsarin da ke tattare wajen kwasan ragunan zuwa birane domin sayarwa.

Asalin hoton, Ouedkniss.com

Bayanan hoto,

'Yadda ake tallar Raguna da Tumaki a Intanet.

Ana sa ran za a yi layya da dabbobi kusan miliyan shida a Algeria a bana, sabanin miliyan hudu da aka yanka a shekarun baya.

Kungiyar manoma ta Algeria ta ce tana son sawwake wa mutane dabbobin layya inda za su iya saya cikin sauki.

A ranar 21 ga watan Agusta ake sa ran gudanar da Eid al Adha, biki na biyu mafi muhimmaci ga Musulmi bayan bikin Sallar Azumi wato Eid el-Fitr.