Ana zabe cikin matakan tsaro a Mali

Zaben Mali

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Al'ummar Mali na zabe cikin fargabar tsaro

Al'ummar Mali na gudanar da zaben shugaban kasa zagaye na biyu mai cike da kalubalen tsaro.

A wannan karon ma za a fafata ne tsakanin shugaba mai ci Ibrahim Boubakar Keita da ke neman wa'adi na biyu da kuma shugaban adawa Soumaila Cisse.

Shugaba Keita ne ya zo na farko a zagayen farko da kashi 42 cikin 100 na yawan kuri'u fiye da Cisse tsohon ministan kudin kasar wanda ya samu kashi 18 cikin 100 na kuri'un.

Ana zagaye na biyu na zaben ne cikin yanayi na barazanar tsaro bayan rikici ya mamaye zagayen farko.

Da misalin karsfe takwas na safe agogon GMT ake sa ran bude runfunan zabe yayin da kuma ake sa ran rufe wa da misalin karfe shida na yamma.

An dai samu karancin fitowar masu kada kuri'a a zagayen farko inda kashi 40 ne kawai suka fito daga cikin kashi dari na yawan adadin masu kada kuri'a.

Rikicin da aka samu a zaben zagayen farko na shugaban kasa da aka gudanar watan jiya ya sa gwamnatin Mali kara yawan dakaru domin wanzar da tsaro a runfunan zabe.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Sojoji kimanin 36,000 gwamnatin Mali ta ce za ta girke domin zaben, inda aka kara yawan dakaru 6,000 fiye da adadin wadanda aka girke a zagayen farko.

Kusan kashi uku na masu kada kuri'a ne rikicin ya hana wa kada kuri'a a zagayen farko bayan rikicin ya hana bude runfunan zabe kusan 900.

Mali na fuskantar barazanar hare-hare ne daga arewaci da kuma tsakiyar kasar.

Ministan tsaron kasar Salif Traore ya shaidawa BBC cewa za su tsaurara tsaro a yankin tsakiyar kasar da aka samu matsaloli a zagayen farko.

Saboda matsalar tsaron ne dai ya sa 'yan takarar zaben na shugaban kasa suka takaita yakin neman zabensu a Bamako babban birnin kasar.

Alamomin nasara

Ana dai ganin shugaba Bubakar Keita ne zai yi nasara a zaben bayan samun yawan kuri'u a zagayen farko duk da suka da yake fuskanta daga abokin takararsa Cisse kan gazawa wajen shawo kan matsalar tsaron da kasar ke fama da ita.

'Yan takarar da suka zo na uku da na hudu a zagayen farko da aka gudanar sun ki marawa Cisse tsohon ministan kudin kasar baya, wani babban kalubale gare shi akan shugaba Keita a zaben.

Tun kafin zaben na zagaye na biyu Kotun kundin tsarin mulki ta yi watsi da zargin da 'yan adawa suka shigar kan an yi magudi a zagayen farko.

Barazanar mayakan jihadi a Mali dai ta bazu daga yankin arewaci zuwa tsakiya da kudancin kasar har zuwa kasashe makwabta, wanda wannan ne babban kalubalen da ke gaban sabon shugaban da za a zaba, Musamman wajen tabbatar da yarjejeniyar 2015 da aka kulla tsakanin gwamnati da 'yan tawaye.