An jinkirta bikin rantsar da zababben shugaban kasa a Zimbabwe

Emmerson Mnangagwa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Hukumar zabe a Zimbabwe ta ayyana shugaba Emmerson Mnangagwa a matsayin wanda yayi nasara a zaben na 30 ga watan Yuli

An dage bikin da aka shirya gudanarwa a yau Lahadi na rantsar da shugaba Emmerson Mnangagwa a matsayin sabon shugaban Zimbabwe.

Wannan matakin na bangaren 'yan adawa ya biyo bayan rashin amincewa da sakamakon zaben da suka yi ne, inda suka shigar da kara a gaban kotu.

Jagoran jam'iyyar adawa ta MDC, Nelson Chamisa, ya ce suna da hujjoji da ke cewa an kwace masa nasara ne a zaben shugaban kasa na 30 ga watan Yuli.

Jam'iyyarsa ta kuma ce "an tafka gagarumar satan kuri'u da magudi", amma hukumar zaben kasar ta kafe cewa ba a aikata irin wannan laifi ba.

Mista Mnangagwa ya lashe zaben da kashi 50.8 cikin 100 na kuri'un da aka kada, shi kuma Mista Chamisa ya sami kashi 44.3 cikin 100.

Ministan shari'a Ziyambi Ziyambi ya bayyana cewa "an dakatar da bikin rantsar da shugaban kasa kamar yadda aka shirya", bayan da jam'iyyar MDC ta kalubalanci sakamakon zaben a kotu a ranar Jumma'a.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Jagoran jam'iyyar adawa ta MDC Nelson Chamisa ya ce an sace zaben da yayi nasara ne

Al'ummar Zimbabwe ta yi ta fatan wannan karon za a sami kwanciyar hankali da sauyi mai dorewa bayan shekaru 37 na mulkin hambararren shugaba Robert Mugabe.