APC ta lashe zaben dan majalisa a Kogi

Voters line up to cast their ballots in an election in Nigeria

Asalin hoton, Getty Images

Hukumar zabe ta Najeriya INEC ta bayyana dan takarar jam'iyyar APC mai mulkin kasar a matsayin wanda ya lashe zaben na majalisar wakilai na mazabar Lokoja/Kogi Koton-Karfe.

Farfesa Rotimi Ajayi na sashin nazarin kimiyyar siyasa na Jami'ar gwamnatin Tarayya ta Lokoja ne ya bayyana sakamakon.

Ya bayyana Haruna Isa na dan jam'iyyar APC, wanda ya sami kuri'u 26,860 a matsayin wanda ya lashe zaben:

"Haruna Isa ya cika dukkan sharuddan zabe, kuma hi ne ya sami kuri'u mafi yawa, saboda haka shi ne ya lashe zaben dan majalisar da ya gudana."

An gudanar da zaben ne don maye gurbin dan majalisar wakilai na mazabar Lokoja/Kogi Koton-Karfe wanda wata babbar kotu ta sauke daga mukamin.

Dan takarar APCn ya fafata ne da wasu 'yan takara su takwas daga jam'iyyu daban-daban.

Mai bi masa shi ne Abubakar B. Muhammad na jam'iyyar PDP wanda ya sami kuri'u 14,845.

Sai kuma Muhammad Kazeem na jam'iyyar ADC wanda shi kuma ya sami kuri'u 2,984.

An dai gudanar da zabuka guda hudu na maye gurbi a wasu mazabu dake ciki tarayyar Najeriya a jiya Asabar.

Mazabun sune na sanatoci a Arewacin Katsina da Kudancin Bauchi da na dan majalisar wakilai a mazabar Lokoja/Kogi Koton-Karfe na jihar Kogi.

Akwai kuma zaben maye gurbin dan majalisar jiha a mazabar Obudu ta jihar Kuros Riba.