PDP ta lashe zaben Kuros Riba

Voting in process in Nigeria

Asalin hoton, Getty Images

Dan takarar jam'iyyar PDP ya lashe zaben maye gurbi na mazabar Obudu, inda ya doke sauran 'yan takara daga jam'iyyu hudu.

Dan takarar jam'iyyar PDP, Abbey Awara Ukpukpen ya lashe zaben da kuri'u 12, 712.

Ya doke sauran 'yan takarar da suka fafata da shi, ciki har da na jam'iyyar APC wanda ya sami kuri'u 4,345.

An dai gudanar da zabuka guda hudu na maye gurbi a wasu mazabu dake ciki tarayyar Najeriya a jiya Asabar.

Mazabun sune na sanatoci a Arewacin Katsina da Kudancin Bauchi da na dan majalisar wakilai a mazabar Lokoja/Kogi Koton-Karfe na jihar Kogi.

Akwai kuma zaben maye gurbin dan majalisar jiha a mazabar Obudu ta jihar Kuros Riba.