Birtaniya ta tura sojojinta aikin hajji

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Birtaniya na son mabiya addina daban-daban su shiga rundunar sojan kasar.

A wani yunkuri na kokarin janyo wasu mabiya addinai su shiga rundunar sojan Birtaniya, rundunar ta dauki nauyin tura wasu sojojinta musulmi zuwa aikin hajjin bana a kasar Saudiyya.

Wannan ne karo na hudu na rundunar ta sojan Birtaniya ke tura sojoji Makka domin aikin hajjin, wanda daya ne daga shikashikan musulunci biyar.

Sojan kasar ta Saudiya ne za su yi wa takwarorinsu na Birtaniya masaukin baki.

A iya cewa dai wannan wani lokaci ne da sojojin za su tafi wata kasa domin aikin ibada, ba don yaki ba ko kuma bada horo.

Da dama daga sojojin sun je wasu kasashe a fadin duniya domin yi wa kasarsu da Sarauniya aiki.

To sai dai wannan karon za su yi tafiyar ne domin aikin ibada, da kuma cika shikashikan addininsu.

Lamarin ya faranta ran sojojin

Sojojin da suka samu wannan dam dai sun bayyana farin ciki.

Daya daga sojojin da za su sauke faralin a bana kofur Fatou Singhateh tace ta ji dadin wannan dama da ta samu.

"Wannan babban abu ne a gareni, saboda aikin Hajji na daya daga shikashikan musulunci da ya zama wajibi mu muslmi mu sauke. Don haka zuwa hajjin nan ina cikin farin ciki, ina matukar murna," in ji Fatou.

Shi ma wani sojan wanda likita ne kuma kwamanda Mansoor Khan ya ce abin farin ciki ne a ce zai je ya ya yi sallah tare da dubban musulami.

"Waje ne da za ka je ka hadu da miliyoyin musulmi, kuna yin komai iri daya, ba tare da tunanin wani abin duniya ba. Kawai kuna tare kuma sallah", a cewar kwamanda Mansoor.

A yanzu dai yawan musulmi a sojojin Birtaniya bai kai kaso daya cikin dari ba, to sai dai rundunar sojan na son kara jan hankalin musulmi su shiga aikin soja.

Kuma wannan ne ya sa a farkon wannan shekara aka kaddamar da wani kamfe don jan hankalin musulmi.

Wani limamin sojojin Ali Omar ya ce tunanin wasu musulmi na cewa ba za su iya gudanar da addininsu ba idan suka shiga soja, shi ne ya ke hana su shiga aikin sojan a Birtaniya.

To amma limamin ya ce sam ba haka lamarin ya ke ba.

Ya ce "Rundunar sojan Birtaniya ta dauki limamai, kuma ni ma ina daya daga cikin limaman sojoji, domin tabbatar da cewa an kula da bukatun su na addini", kamar yadda Liman Ali ya bayyana.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Za a tura sojojin Birtaniya ne Saudiya domin aikin Hajji, ba kamar wannan sojan da aka tura Iraki domin yaki ba.

Labarai masu alaka