Za a biya Musulmar da ta ki yin hannu da namiji diyya

Farah Alhajeh Hakkin mallakar hoto Farah Alhajeh
Image caption Farah Alhajeh ta ce ta dauki wannan mataki ne saboda matan da suka fuskanci makamanci irin wannan matsalar su fito su neman hakkin su.

Wata Musulma 'yar kasar Sweden ta samu nasara a kotu kan karar da ta shigar saboda an ki daukanta aiki, sakamakon kin yin hannu da wani namiji lokacin da aka yi mata jarrabawar daukar aiki.

Farah Alhajeh mai shekara 24, tana neman aikin fassara ne a wani kamfani, lokacin da ta ki amincewa ta gaisa da mutumin da ke jagorantar jarrabawar daukar aiki saboda dalilan addini.

Ta kuma noke hannuta a madadin gaisuwar.

Kotun ma'aikata a kasar ta yanke hukuncin cewa an nuna wa Farah bambanci, kuma ta umarci kamfanin da ya biyata diyyar dala 4,350

Akasari Musulmi kan gujewa hada jiki ko irin wannan gaisuwa da mutumin da ba muharaminsu ba.

Sai dai mika hannu a lokacin gaisuwa al'ada ce ta kasashen Turai. Akwai yiwuwar dokar yaki da wariya ta haramta wa kamfanoni da ma'aikatun gwamnati nuna bambanci saboda dalilai na jinsi.

Ofishin da ke yakar nuna irin wannan wariya a Sweden, wanda ya wakilici Farah a kotu, ya ce hukuncin ya yi la'akari da bukatun masu daukar aiki, da 'yancin mutum, da kuma muhimmaci da 'yancin kare addini.

Menene dalilan yanke wannan hukunci?

Kamfanin da ke Uppsala mahaifar Farah, ya ce ya haramtawa ma'aiakatansa nuna bambanci tsakanin mata da maza, amma bai amince ma'aikaci ya ki mika hannu akan dalilan jinsi ba.

Sai dai lauyan da ke kareta ya ce, ta yi kokarin gudun baccin-rai, shiyasa ta noke hannuta ta kuma dafe kirjinta a matsayin girmamawa ga mata da maza.

Kotun ta kuma samu kamfanin da kokarin yin adalci tsakanin mata da maza, amma ya yi biris da batun da ya shafi mika hannu a gaisa.

Farah ta samu goyon baya da kariya daga Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Tarayyar Turai akan matsayarta.

Kungiyar ta ce tsarin kamfanin akan gaisuwa bai dace da addinin Musulminci ba.

Kotun ta kuma nuna rashin amincewarta da korafin Kamfanin cewa, yanayin gaisuwar Farah matsala ce ta wata fuskar.

An dai samu rabuwar kawunan tsakanin alkalai a shari'ar-inda uku suka nuna goyon baya, biyu kuma suka nuna adawarsu.

MeFarahke cewa?

Bayan hukuncim, Ms Farah ta shaidawa BBC cewa tayi amanna cewa abu ne mai muhimmacin ''kar ka mika-kai'' in dai kana kan da gaskiyar ka, koda ba ka da rinjaye.

''Na yarda da Allah, ba kasafai ake samun haka a Sweden ba...kuma ba zan yi kasa a gwiwa ba, kuma ba zan cutar da kowa ba,''inji Farah.

''A kasa ta...Babu yadda za a yi ka nuna bambanci tsakanin mata da maza. Ina daraja hakan. Shiyasa bana hada jiki da namiji ko mace. Ina rayuwarta akan koyarwar addinina, hakazalika ina kuma bin dokokin kasar da na ke zaune,'' a cewar Farah.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Hada hannu tsakanin maza da mata yayin gaisawa ya zama ruwan dare a nahiyar turai, sai dai ba kowa ne ke hakan ba.

Labarai masu alaka

Karin bayani