An kori jami'an gwamnati kan badakkalar maganin rigakafin jarirai

Food and Drug Administration officials check on vaccines for rabies at the Disease Control and Prevention Center in Huaibei in China

Asalin hoton, Getty Images

An kori wasu manyan jami'an gwamnati masu yawa a sanadiyyar wata matsalar gurbatattun magungunan rigakafi a China da ta ki-ci-ta-ki-cinyewa.

Kimanin jami'ai 40 kuma na fuskantanr matakan ladabtarwa, kuma rahotanni na cewa kamfanin da ake tuhuma ya sayar da nunkin yawan magungunan rigakafi da akan ba jarirai a kasar.

Hukumar da ke kula da ingancin magunguna ta China ta ce kamfanin Changsheng Biotechnology ya sayar da nunkin magungunan rigakafi na ciwon tarin fika da na tetanus.

Magungunan rigakafin da ake magana akai sun zarce 500,000 a halin da ake ciki.

Tuni dai aka kama shugaban kamfanin da wasu mutum 14 a dalilin wannan badakkalar.

Kana wasu jami'an gwamnati da ke da alhakin sa ido kan batutuwan tsaftace abinci da magunguna sun rasa ayyukansu, ciki har da mataimakin gwamnan yankin Jilin na kasar.

Kawo yanzu ba a sami rahotannin cewa wasu jarirai sun sami wani lahani bayan shan wadannan magungunan ba, amma batun ya tayar da hankulan 'yan kasar game da ingancin magunguna a kasar ta China.

Kafofin watsa labarai mallakin gwamnati sun ruwaito cewa fiye da jami'an gwamnati 40 ne ke fuskantar matakan ladabtarwa a sanadiyyar wannan lamarin.