Wadanne batutuwa Shugaba Buhari zai taras a Nigeria?

  • Nasidi Adamu Yahya
  • BBC Hausa
Muhammadu Buhari

Asalin hoton, Getty Images

Ranar Asabar ake sa ran shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai koma kasar bayan ya kwana goma yana hutun aiki.

Shugaban ya tafi birnin Landan ne bayan ya soma hutun ranar uku ga watan Agusta.

Gabanin tafiyar tasa, ya mika ragamar gudanar da kasar a hannun mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo.

A farkon wannan makon ne wasu jaridun kasar suka bayyana cewa shugaban ya dage ranar da zai koma Najeriya, sai dai mai taimakawa shugaban na musamman kan yada labarai Malam Garba Shehu ya tabbatar wa BBC cewa a ranar Asabar Shugaba Buhari zai koma gida.

Abubuwa da dama sun faru a kasar tun bayan yin bulaguron Shugaba Buhari:

An yi wa majalisar dokoki kutse

Asalin hoton, Twitter/NASS

Jim kadan da ficewar Shugaban daga Najeriya ne dai, wato ranar bakwai ga watan na Agusta aka wayi gari da ganin wasu jami'an hukumar tsaro ta farin kaya, DSS, a babbar kofar shiga majalisar dokokin tarayya.

Jami'an, wadanda kafofin watsa labarai suka nuna sanye da hulunan da suka rufe fuskokinsu, sun hana kowa shiga majalisar - ciki kuwa har da 'yan majalisar dokokin.

Wasu 'yan majalisar dokokin na jam'iyyar PDP mai hamayyar, wadanda tunda sanyin safiya suka isa ginin majalisar duk da yake suna hutu, sun yi zargin cewa an aika jami'an DSS ne domin su ba da kariya ga takwarorinsu na jam'iyyar APC mai mulki wadanda, a cewar su, ke cikin zauren majalisar domin su tsige shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki.

Daga bisani dai 'yan majalisar na APC sun musanta zargin.

An cire shugaban DSS

Asalin hoton, www.dailytrust.com.ng

Wannan kutse da aka yi wa majalisar dokokin ta Najeriya, wanda ya dauki tsawon sa'o'i da dama, ya jawo muhawara da suka daga bangarori daban-daban, ciki har da tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar.

Masu sukar sun zargi bangaren zartawa da yunkurin kassara mulkin dimokradiyya.

A tsaka da wannan kwamacala ne fadar shugaban kasar ta fitar da sanarwar sauke shugaban DSS, Lawan Daura, daga kan mukaminsa.

An nada Mr Matthew B. Seiyefa a matsyin shugaban-riko na DSS.

Mukaddashin shugaban kasar ya ce matakin yi wa majalisar dokoki kutse ya sabawa doka kuma abin kyama ne.

'Yan kasar da dama sun yi murnar cire shugaban na DSS, wanda ake zargi da take hakkin bil adama da kin bin umarnin kotu, daga kan mukaminsa.

Saraki ya 'gagari' gwamnatin Buhari

Asalin hoton, Twitter/NASS

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Kwana guda bayan soke shugaban hukumar tsaro ta farin kaya daga kan mukaminsa ne shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ya gudanar da abin da ya kira taron manema labarai na duniya inda ya caccaki yunkurin da aka yi "na cire ni daga kan mukamina."

Saraki ya yi zargin cewa an yi yunkurin cire shi ne saboda ficewar da shi da wasu 'yan majalisar suka yi daga jam'iyyar APC zuwa jam'iyyar PDP.

A cewar sa, jagorancin majalisar bai dada shi da kasa ba amma ba zai sauka daga kujerarsa kamar yadda shugaban jam'iyyar APC ya nemi ya yi ba sai dai idan kashi biyu cikin 'yan majalisar dattawan ne suka cire shi - kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya bayyana.

Wadannan kalamai dai na ci gaba da yi wa APC zafi, inda shugabanta Adams Oshimohle ya jaddada cewa ko da karfin tuwo sai Sanata Saraki ya sauka daga mulki- ko da yake daga bisani ya ce za su bi doka wurin cire shi.

Jam'iyyar APC ta samu karuwa

Da alama daya daga cikin abubuwan da za su faranta ran Shugaba Buhari idan ya koma Najeriya shi ne karuwar da jam'iyyarsa ta APC ta samu.

A ranar Asabar, 11 ga watan Agusta ne aka gudanar da zaben maye gurbin kujerun majalisar dattawa a jihar Katsina, mahaifar shugaban kasar da kuma jihar Bauchi.

Shugaban ya yaba wa al'umar jihohin biyu, yana mai cewa "zaben da kuka yi wa APC ya nuna cewa za ku ci gaba da amincewa da mu."

Sakamakon zaben ya nuna cewa jam'iyyar APC ce ta lashe dukkan su - hakan na nufin APC ta karfafa rinjayen da take da shi a majalisar dattawa duk da ficewar da wasu 'yan majalisar dokokin suka yi daga cikin ta makonnin da suka wuce.

Aisha Buhari ta samu Digirin Digirgir

Asalin hoton, InSTAGRAM/Aisha Buhari

Bayanan hoto,

Aisha Buhari ta sha sukar mijinta

Kazalika wani abin farin cikin da Shugaba Buhari zai taras shi ne karramawar da wata Jami'ar Koriya ta Kudu ta yi wa mai dakin shugaban kasar Aisha Buhari ta yi.

Jami'ar Sun Moon ta bai wa matar shugaban kasar Digirin Digirgir a fannin gudanarwa.

Osinbajo ya yi wa rundunar 'yan sanda garambawul

Asalin hoton, POLICENG_PCRRU/TWITTER

A tsakiyar makon nan ne kuma mukaddashin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya yi wa bangaren rundunar 'yan sandan kasar da ke yaki da 'yan fashi da makami kwaskwarima.

Rundunar ta SARS, kamar yadda aka fi sanin ta, ta yi kaurin suna wurin cin zarafin dan adam da musgunawa da kuma kisa, kamar yadda ake zarginta.

'Yan kasar da dama sun yaba kan daukar wannan mataki - kuma hakan ta sa suna ci gaba da yabawa mukaddashin shugaban kasar - wanda suke gani ya fi Shugaba Buhari gaggawar daukar mataki domin ganin ci gaban kasar.

Sai dai magoya bayan Shugaba Buhari sun sha cewa Farfesa Osinbajo yana daukar dukkan matakan ne tare da masaniyar shugaban kasa - ko da kuwa yana hutu ne.

Ga karin wasu labarai da za ku so ku karanta: