Tsohon shugaban majalisar dinkin duniya Kofi Annan ya rasu

Mr Annan ya wa'adi biyu a shugabancin majalisar dinkin duniya tsakanin shekarun 1997 da 2006

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Mr Annan ne bakar fata na farko da ya shugabanci majalisar dinkin duniya

Tsohon shugaban majalisar dinkin duniya Kofi Annan ya rasu yana da shekara 80 a duniya.

Wata sanarwa da gidauniyar the Kofi Annan Foundation ta fitar ta ce Mr Annan ya rasu ranar Asabar bayan ya yi fama da gajeriyar rashin lafiya.

Ta bayyana shi a matsayin "dattijon duniya baki daya wanda ya mayar da hankali wurin fafutikar ganin an yi wa kowa adalci da samar da zaman lafiya a duniya".

Babban ma'aikacin diflomasiyyar, wanda dan asalin kasar Ghana ne, ya mutu ne a birnin Geneva, inda ya kwashe shekara da shekaru yana zama.

Annan ne bakar fata na farko da ya zama shugaban majalisar ta dinkin duniya, inda ya yi wa'adi biyu tsakanin shekarun 1997 da 2006.

Daga bisani ya zama wakilin majalisar dinkin duniya na musamman a Syria, inda ya jagoranci yunkurin wanzar da zaman lafiya a kasar.

Marigayin ya shugabanci majaliar dinkin duniya ne a daidai lokacin da aka soma yakin Iraki da kuma barkewar annobar cutar HIV/Aids.

Mr Kofi Annan ya taba lashe kyautar lambar yabo ta Nobel kan zaman lafiya a 2001.

Kofi Annan ya bayyana cewa babbar nasarar da ya yi a duniya ita ce ta samar da shirin nan na Ci gaban Muradun Karni - wanda ke da zummar rage talauci da mutuwar kananan yara.

Sai dai ya sha suka a wasu bangarori. Masu sukar tasa sun caccake shi saboda gazawar majalisar dinkin duniya wurin tsayar da kashe-kashe kare-dangi a Rwanda a shekarun 1990 lokacin da yake shugabantar hukumar tabbatar da zaman lafiya ta majalisar.