Rashin musabaha ya sa an ki bai wa Musulmi damar zama 'yan kasa

Musabaha

Asalin hoton, Science Photo Library

Bayanan hoto,

Ma'auratan sun ki yin musabaha da mutanen da ba jinsinsu ne ba

Jami'ai a Switzerland sun ce an hana wasu ma'aurata Musulmi izinin zama 'yan kasar saboda sun ki amincewa su yi musabaha da jinsin da ba nasu ba lokacin da suka je ganawa.

Jami'an sun bayyana daukar wannan mataki ne ranar Juma'a, suna masu cewa ma'auratan sun gaza yin biyayya ga tsarin kasar na daidaiton jinsi.

Ma'auratan, wadanda aka yi wa tambayoyi kan bukatar da suka shigar ta neman zama 'yan kasar watannin da suka wuce, sun yi ta fama kafin su amsa tambayoyi daga wadanda ba jinsinsu ba ne.

Kwanaki kadan da suka gabata, wata Musulma 'yar kasar ta Switzerland ta yi nasarar samun diyya bayan da aka hana ta kammala rubuta jarabawar neman aiki saboda ta ki yin musabaha da mutanen da ba jinsinta ne ba.

Hukumomin Switzerland sun ce dole ne duk wanda ke son zama dan kasar ya dace da halaye da zamantakewa irin na 'yan kasar.

Basu yi karin bayani kan ma'auratan ba - kafofin watsa labaran kasar sun ce sun fito ne daga Arewacin Afirka - sai dai sun ce ma'auratan sun gaza cika sharudan zama 'yan kasar saboda sun nemi izinin zama ne daga birnin Lausanne.

Magajin birnin Lausanne, Gregoire Junod, ya shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP an bai wa kowa 'yancin yin addini amma 'yancin "ba zai wuce na zama dan kasa ba."