Duniya na alhinin mutuwar Kofi Annan

Mr Annan

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

An dauki hoton Mr Annan ne wata guda kafin mutuwar sa.

Shugabannin kasashen duniya da 'yan siyasa da kuma jami'ai daga bangarori daban-daban na duniya na alhinin mutuwar tsohon shugaban majalisar dinkin duniya, Kofi Annan.

Mr Annan ya rasu ne ranar Asabar bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya, a cewar Gidauniyar the Kofi Annan Foundation.

Babban ma'aikacin diflomasiyyar, wanda dan asalin kasar Ghana ne, ya mutu ne a birnin Geneva, inda ya kwashe shekara da shekaru yana zama.

Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo ya mika ta'aziyyarsa ga iyalai da 'yan uwan Mr Annan bisa wannan babban rashi da duniya ta yi.

A cewar sa, tsohon shugaban majalisar dinkin duniyar ya "ya daukaka sunan kasarmu sabida mukamin da ya rike da kuma halayensa a duniya. Shi mutum ne da da ya yi amanna cewa duk dan kasar Ghana zai iya zama abin da yake son zama idan ya zage damtse."

A nasa bangare, shugaban majalisar dinkin duniya, António Guterres, ya ce Kofi Annan "mutum ne da ya jagoranci samar da abubuwa masu kyawu. Na bi sahun duniya wajen alhinin rashin sa. Nasarorin da ya samu wajen samar da zaman lafiya za su zamar mana abin koyi a wannan duniya mai cike da rudani."

Ita ma firai ministar Burtaniya Therese May ta bayyana bakin cikinta bisa rasuwar Mr Annan, tana mai cewa "shugaba ne na gari wanda ya kawo sauyi a majalisar dinkin duniya, ya kawo gagarumar gudunmawa domin ganin an samun ingantacciyar duniya sannan ya bar duniya fiye da yadda ya taras da ita."

A sakon da shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Bukola Saraki, ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce marigayi Kofi Annan "mutum ne jajirtace wanda ya kasance mai kare hakkin mutanen da ba su da galihu, kuma ma'aikacin diflomasiyya ne wanda ya yi aiki tukuru domin samar da zaman lafiya a wannan duniya mai cike da matsaloli."

Takwaransa na majalisar wakilai, Yakubu Dogara, ya bayyana cewa duk da yake kowa ya san zai mutu, amma har yanzu mutuwa bakuwa ce a duk lokacin da ta faru.

A cewar sa, gudunmawar Mr Kofi Annan ya bayar wajen inganta rayuwar dan adam ba za ta misaltu ba.

Hamshakin attajirin nan da ya fi kowa kudi a Afirka, Alhaji Aliko Dangote, ya mika ta'aziyyarsa ga iyalan Kofi Annan, inda ya ce marigayin mutum ne "da ya kware wurin shigewa gaba doin samar da zaman lafiya da adalci da daidaito a duniya. Duniya ta yi rashin babban mutumin da ke kaunar zaman lafiya."

Shi ma gwamnan jihar Bauchi, Mohammed Abdullahi Abubakar ya ce "Nahiyar Afirka ta yi rashin daya daga cikin manyan 'ya'yanta, kuma duniya ta yi rashin mutumin kirki."

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Alhaji Atiku Abubakar marigayi Mr Kofi Annan ya bar Kofi Annan "ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen ci gaban dan adama kuma ba za a taba mantawa da shi ba."