Buhari ya yi ta'aziyyar rasuwar Kofi Annan

Muhammadu Buhari

Asalin hoton, NIGERIA PRESIDENCY

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana jajensa bisa mutuwar tsohon shugaban majalisar dinkin duniya Mr Kofi Annan.

Mr Annan ya rasu ne ranar Asabar bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiyar, in ji wata sanarwa da Gidauniyar the Kofi Annan Foundation ta fitar.

A sanarwar da mai magana da yawun shugaban kasar Femi Adesina ya fitar, ya ambato Shugaba Buhari yana mika ta'aziyyarsa ga shugaba da al'umar kasar Ghana - mahaifar Mr Annan.

A cewar sanarwar, "Shugaba Buhari, wanda ya kira shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo ta wayar tarho daga London, ya mika alhinin 'yan Najeriya da kasashen ECOWAS member, ganin irin muhimmancin marigayin a harkokin kasashen duniya da kuma hangen nesansa na sauya Yammacin Afirka da ma nahiyar baki daya."

Shugaba Buhari ya kara da cewa marigayi Mr Annan mutum ne mai dattako da kaunar jama'a da kankan da kai, abubuwan da suka sanya shi yin zarra a duniya

Shugaban nan Najeriya ya kuma jinjinawa marigayi Mr Annan musamman a kokarin da ya yi na yaki da HIV/Aids a Afirka da kuma kaddamar da Muradun ci gaban Karni.

Ya yi addu'ar Allah ya bai wa iyalai da 'yan uwansa hakurin rashinsa.