Akshay Kumar shi ya fi mabiya Instagram a Bollywood

Akshay Kumar Hakkin mallakar hoto Entrepreneur

Shahararren jarumin fina-finan Bollywood Akshay Kumar, ya zama na farko da ya fi sauran jaruman fina-finan Indiya samun masu bibiyarsa a shafin sada zumunta na Instagram.

A yanzu haka Akshay na da masu bibiyarsa da suka kai miliyan 20.

A ranar Litinin 20 ga watan Augusta, 2018, shafin Instagram ya ba wa Akshay lambar yabo saboda kai wa wannan mataki.

A shafinsa na Instagram, Akshay Kumar ya rubuta cewa, ' Wannan wata sabuwar dama ce da na samu daga mutane masu kima a Instagram. Ina mai farin cikin sanar da ku cewa na zamo jarumin Bollywood namiji na farko da na ke da masu bibiyata a Instagram miliyan 20.Nagode wa masu bibiyata kwarai da gaske.'

A cikin watan Augustan 2018, an saki fim din Akshay Kumar mai suna Gold da ya samu gagarumar karbuwa.

Waye Akshay Kumar?

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Akshay Kumar na daga cikin jaruman fina-finan Indiya da suke tashe, saboda irin fina-finan da ya ke, da kuma rawar da ya ke takawa a ciki.

An haife shi a ranar 9 ga watan Nuwambar 1967, wato yanzu haka ya na da shekara 51 ke nan.

Ya fara fitowa a fim a shekarar 1991 a fim din Saugandh.

Daga na kuma ya ci gaba da fitowa a fina-finai.

Akshay, ya yi manyan fina-finai da suka samu karbuwa ba ma a kasar Indiya kadai ba, har ma da wasu kasashen duniya.

Daga cikin fina-finan sa akwai, PadMan da Toilet: Ek Prem Katha da Main Khiladi Tu Anari da Sapoot da Rustom da Waqt: The Race Against Time da kuma Aitraaz.

A kan yi masa lakabi da Mr Khiladi, kasancewar ya yi fina-finai da suke dauke da sunan Khiladi da dama.

Hakkin mallakar hoto India Today

Yanzu haka yana auren jaruma Twinkle Khanna inda suke da 'ya'ya biyu, wato mace da namiji.

Akshay, ba wai jarumi ne kawai ba, ya kan shirya fim ma wato furodusa.

Karanta wasu karin labaran

Labarai masu alaka