Musulman duniya na bikin babbar Sallah

Eid el Adha Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An kwadaitar wa Musulmi yin layya domin koyi da Manzo SAW

Al'ummar Musulmi a fadin duniya na gudanar da bukukuwan sallar layya.

Bikin da ake kira na babbar Sallah na zuwa ne kwana guda bayan miliyoyin Musulmin da suka je aikin Hajji sun yi hawan Arafa a jiya litinin.

Wani muhimmin abu yayin wadannan bukukuwa na yau shi ne yin layya.

Bayan kammala sallar idi musulmai masu hali za su yanka dabbobin layya.

Sheikh Hussaini Zakariyya wani malamin addinin Musulunci a Najeria ya ce babban amfanin layya shi ne koyi da Annabi SAW.

Malamin ya ce ana son wadanda suka samu halin yin layyar, su taimaka wa wadanda ba su samu ikon yi ba da naman da suka yanka na layya.

Babbar sallah ko sallar layya, rana ce ta biki da murna da shagali, don kuwa ko ba komai, an shekara da rai.

Kuma a ranar Sallah akan yi ziyara ga `yan uwa da abokan arziki, tare da rarraba abinci don kara dankon zumunci.

Labarai masu alaka