Musulmi sun yi rokon ruwa ranar Sallah

Muslims pray in Sydney at the Lakemba mosque Hakkin mallakar hoto Lebanese Muslim Association
Image caption Dubban mutane ne suka halarci sallar Idi a Sydney

Kimanin Musulmin Australia 30,000 ne suka taru a birnin Sydney ranar Talata inda suka yi sallar rokon ruwa sakamakon mummunan farin da ba a taba fuskantar irin sa ba a kasar.

Masallata daga manyan masallatai 16 ne suka hadu wuri guda "domin nuna goyon baya da ba da hadin kai" ga manoma da sauran mutanen da farin ya shafa.

An yi sallar ne lokacin da aka gudanar da babbar sallah sannan aka yanka dabbobi.

An kaddamar da wata gidauniyar tallafa wa manoman da farin ya shafa.

Kungiyar Musulmi 'yan kasar Lebanon da ke masallacin Lakemba na yammacin Sydney ce ta kaddamar da gidauniyar.

"A matsayinmu na 'yan uwa daya 'yan kasar Australia, muna ganin ya kamata mu bayar da tamu gudunmawar da goyon baya ga mabukata," in ji shugaban kungiyar Samier Dandan.

"Wannan ne lokacin da ya kamata mu hada kai mu tallafawa wadanda ke cikin mawuyacin hali."

Hakkin mallakar hoto LMA
Image caption An yi sallar rokon ruwan ce a masallacin Lakemba da ke yammacin Sydney

Daraktan kungiyar, Ahmad Malas, ya shaida wa BBC kowa ya ji dadi lokacin da aka kaddamar da gidauniyar.

Ya kara da cewa ana yin sallar rokon ruwa ce idan ana kamfar ruwan sama.

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Manoma na fuskantar matsala wurin shayar da dabbobinsu

Labarai masu alaka