UNICEF ya yi gargadi kan makomar yaran Rohingya

Sansanin 'yan gudun hijirar Rohingya a Bangladesh

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Sansanin 'yan gudun hijirar Rohingya a Bangladesh

Asusun kula da yara kanana na Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadi kan makomar ilimin 'ya'yan 'yan gudun hijirar Rohingya da ke rayuwa a Bangladesh.

Asusun ya ce sama da yara 500,000 na kabilar Rohingya da ke zaune a sansanin 'yan gudun hijira a Bangladesh ne ba sa zuwa makaranta tare da gargadi cewar idan ba a tallafa musu ba suna cikin hadarin dodewar basira.

Unicef ya ce yaran Rohingya 140 ne kadai ke zuwa makaranta a sansanonin da suke zaune a Bangladesh.

UNICEF ta fitar da rahoton ne a daidai lokacin da aka cika shekara guda da rikicin da ya yi sanadiyyar mutuwar daruruwan tsirarun musulmi na kabilar Rohingya da ake zargin sojin Myanmar da aikatawa a jihar Rakhine.

Rahoton na Unicef ya ce rayuwa da kuma makomar yara kusan dubu dari hudu da ke sansanonin 'yan gudun hijiraa Bangladesh na cikin hatsari, yayin da kuma tallafi ya yanke zuwa ga dubban yaran Rohingya da ke Myanmar

Asusun ya ce Bangladesh ta haramta wa 'yan gudun hijira samun ilimi saboda gwamnati na fargaba kan mutanen na Rohingya yawancinsu musulmi na iya ci gaba da zama a kasar.

Kakakin Unicef ya ce akwai cibiyoyin ilimi da kungiyoyin agaji suka tanadar ga yara 'yan tsakanin shekara uku zuwa 14 amma kuma wadanda suka haura shekarunsu ba su san makomarsu.

Kuma ya ce babu shakka wannan na tattare da babban hatsari ga makomar yaran.

Yawancin 'yan gudun hijirar dai sun tsere ne tsakanin watanni hudu na farmakin sojojin Myamar bayan kai wa sojojin hari a jihar Rakine a watan Agustan 2017.

Kungiyar agaji ta Save the Children ta ce daya daga cikin biyu na yaran Rohingya sun koma marayu wadanda suka tsere zuwa Bangladesh, yayin da kuma wasu sama da 6,000 na yaran ke kula da kansu.