An rufe babbar gadar Lagos

Lagos

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Tsawon gadar ya kai kusan kilomita 12

Gwamnatin jihar Lagos da ke Najeriya ta ce za ta rufe babbar gadar nan mai muhimmanci da ta hada tsibirin Lagos da sauran unguwannin birnin domin binciken ko gadar na bukatar gyara.

Gadar wadda ake kira third Mainaland Bridge za a rufe ta ne na tsawon kwana hudu kamar yadda gwamnati ta yi alkawali.

Kwamishinan ayyuka na jihar Ade Akinsanya ya ce an tanadi jami'an kula da zirga-zirga a sauran hanyoyi domin saukake wa al'umma kai da komawa a birnin.

Gadar mai tsawon kusan kilomita 12 an kaddamar da ita ne a shekarar 19 90, lokacin mulkin tsohon shugaban Najeriya Ibrahim Basamasi Babangida.

Ana kallon gadar a matsayin mai matukar muhimmanci a birnin na Lagos, cibiyar kasuwancin Najeriya.

Matakin dai zai haifar da cushewar motoci a sauran hanyoyin da ma'aikata da 'yan kasuwa za su bi domin isa cikin birnin na Lagos.

Cushewar hanyoyin kuma zai fi shafi ma'aikata da 'yan kasuwa musamman lura da gadar ita hanya mafi sauki ta shiga birnin Lagos.

Wasu mazauna birnin Lagos sun shaida wa BBC cewa dole su sauya lokacin fita sabanin lokacin da suka saba fita saboda tsoron cushewar hanyoyin mota don kaucewa makara zuwa wurin aiki da kasuwa.

Wasu kuma sun ce rufe gadar zai sa masu zirga-zirgar motocin sufuri kara kudi ga fasinja saboda kewayen da za su yi da kuma cunkoso kafin shiga Ikko.