Da gaske Salah da Kane za su koma Madrid?

Salah

Asalin hoton, Getty Images

Dan wasan Liverpool Mohamed Salah da na Tottenham Harry Kane sun ki karfar tayin koma wa Real Madrid bayan kungiyar ta sayar da Cristiano Ronaldo ga Juventus, kamar yadda kafar yada labarai ta (El Pais - in Spanish)ta bayyana.

Watakila dan wasan Tottenham Danny Rose ya karbi tayin koma wa Paris St-Germain, kamar yadda jaridar (Evening Standard) ta ruwaito.

Sai dai kungiyar Tottenham ba ta karbi bukatar nemansa ba a hukumance, a cewar (Talksport)

Manchester City tana duba yiwuwar daukar golan Real Madrid, Keylor Navas, aro, bayan golan kungiyar Claudio Bravo ya ji rauni, in ji (AS - in Spanish)

Liverpool da Borussia Dortmund suna zawarcin dan wasan Belgium, Divock Origi, kamar yadda (ESPN) ta bayyana.

Chelsea tana kokarin bai wa dan wasan Ingila, Ruben Loftus-Cheek, baki kan ya ci gaba da zama a kungiyar (Mirror).

Tsohon dan wasan Arsenal, Thierry Henry, zai gana da shugabannin kungiyar Bordeaux game da maganar ba shi mukamin jan ragamar kungiyar, kamar yadda jaridar (Mirror) ta ce.