'Yan jam'iyya sun tumbuke Malcolm Turnbull a matsayin firai minista

From let to right: Malcolm Turnbull, Peter Dutton, Scott Morrison, Julie Bishop Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Daga dama zuwa hagu: Julie Bishop, Scott Morrison, Peter Dutton, da Malcolm Turnbull,

Scott Morrison ne sabon firai ministan Ostreliya bayan da 'ya'yan jam'iyar Conservative suka tumbuke tsohon shugaban jam'iyyar saboda gazawarsa.

Malcolm Turnbull ya sha matsin lamba daga 'yan majalisu daga jam'iyarsa da kuma gazawarsa a daidai lokacin da ake shirin gudanar da zabe.

Sabon firai minista Morrison wanda shi ne ma'ajin jam'iyyar kafin wannan abin ban mamakin, ya lashe wata kuri'a ta cikin gida da kuri'u 45 - 40 inda ya kayar da tsohon ministan cikin gida Peter Dutton.

Mista Turnbull bai ma tsaya takara ba a wannan zaben na cikin gida.

Ya amince da a gudanar da zaben ne bayan da ya fuskanci tsananin matsin lamba daga yawancin 'yan majalisar kasar daga jam'iyyarsa.

A shekara goma da ta gabata, an tumbuke firai ministoci uku na kasar ta wannan hanya.

Kuma a 'yan shekarun nan, ba a taba samun wanda ya taba kai karshen wa'adin mulkinsa na shekara uku a matsayin firai ministan Ostreliya ba.

Labarai masu alaka