Buhari ya gaya wa sojoji kada sassauta wa 'yan ta'adda

Shugaba Buhari Hakkin mallakar hoto NIGERIA PRESIDENCY

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci sojojin kasar da kada su sasauta wa 'yan ta'adda da barayin mutane domin karbar kudin fansa da kuma masu satar dabbobi.

Shugaban ya bayyana haka ne ranar Asabar a filin jirgin saman Katsina lokacin da yake ganawa da sojojin gabanin komawarsa Abuja bayan ya yi hutun babbar sallah a mahaifarsa Daura.

Sojojin na cikin rundunar Operations Sharan Daji da Diran Mikiya wadanda aka aike jihar Zamfara da makwabtan jihohi domin magance matsalar barayin mutane da shanu da kuma 'yan fashi da makami.

Kwanakin baya dan majalisar dattawan da ke wakiltar jihar Zamfara Sanata Kabiru Marafa ya shaida wa BBC cewa masu satar shanu sun kashe kusan mutum 1400 a jihar ta Zamfara cikin shekara biyar.

Kazalika masu satar mutane domin karbar kudin fansa sun kashe mutane da dama a jihohin Kaduna da Katsina da ma jihar ta Zamfara.

Sai dai Shugaba Buhari ya umarci sojojin da kada su bar barayin su sha iska, yana mai nuna gamsuwa bisa aikin da suke yi.

''Na zo nan ne kuma na ji dadin samun damar yin magana da ku domin na bayyana muku gamsuwa ta, a matsayina na babban kwamandan tsaron kasa, bisa aikin da wadannan runduna biyu suke yi. 'Yan Najeriya sun sanya muku ido domin ku tabbatar da tsaro. Abubuwan da suke faruwa a wannan yanki ba su da dadin ji," in ji Shugaba buhari

Ya kara da cewa ''Na yi matukar gamsuwa kan yadda jami'an tsaro ke jajircewa kuma ina so kada ku sassauta kan ayyukan da kuke yi."

Hakkin mallakar hoto NIGERIA PRESIDENCY
Hakkin mallakar hoto NIGERIA PRESIDENCY